• English
  • Business News
Sunday, October 19, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Taiwan Wani Yanki Ne Na Kasar Sin

by CMG Hausa
3 years ago
Taiwan

A kwanakin baya ne, sakataren harkokin wajen Amurka Anthony Blinken ya yi wasu kalamai da suka shafi yankin Taiwan na kasar Sin, kamar yadda ya saba. Idan ba a manta ba, a baya ma ya taba bayyanawa a yayin wata hira da aka yi da shi cewa,wai kasarsa na da kudurin tabbatar da cewa, yankin Taiwan zai iya kare kansa. Sai dai kuma Anthony Blinken, idan bai manta ba, ya bayyana a wani taron manyan jami’an kasashen Sin da Amurka da aka gudanar a karshen watan Oktoban shekarar da ta gabata, cewa Amurka za ta ci gaba da martaba manufar Sin daya tak a duniya”. Don haka, ta yaya mutumin da ke furta irin wadannan kalamai na kwan-gaba-kwan baya, ya dace da zama babban jami’in diflomasiyyar Amurka?

Ya kamata Blinken da sauran jami’an Amurka su fahimci cewa, yanzu haka akwai kasashe 180 a duniya, wadanda suka amince tare da goyon bayan manufar kasar Sin daya tak a duniya, kuma wannan ita ce yarjejeniya ta gaskiya da kasashen duniya suka amince da ita. Batun Taiwan, batu ne da ya shafi harkokin cikin gidan kasar Sin, kana babbar moriyar kasar mai muhimmanci, haka kuma shi ne tushen siyasa na alakar Sin da Amurka, kana jan layi na farko tsakaninsu wanda bai kamata a tsallaka shi ba.

Bugu da kari, dokar nan ta dangantakar Taiwan da Amurka da Amurkar ta kirkita, ta saba alkawurran da Amurkar ta dauka a cikin sanarwoyin hadin gwiwa guda uku da Sin da Amurka suka cimma a tsakaninsu. Idan maye ya manta, to uwar diya ba ta manta ba. A kokarin da kasar Sin ke yi na kara fahimtar da Amurka da ma kasashen duniya game da manufar kasar Sin daya tak a duniya, sanarwar da aka fitar bayan kammala cikakken zaman karo na shida na kwamitin tsakiya na JKS karo na 19, a kwanakin nan, ta bayyana karara cewa, kasar Sin za ta ci gaba da martaba ka’idar kasancewar Sin daya tak a duniya, da kuma matsaya irin wannan da aka cimma a shekarar 1992, wadda ke adawa da ayyukan ’yan aware dake neman ’yancin kai na Taiwan, da tsoma baki daga waje. Wannan ya nuna a fili irin tsayin daka na kasar Sin, da kuma matsayinta na kare ikon mallakar kasa, da cikakkun yankunanta da tsaro da moriyar ci gabanta. Koda a yayin zantawarsa da takwaransa na kasar Amurka Joe Biden ta kafar bidiyo a ranar Talata 16 ga watan Nuwanban shekarar 2022, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana matsayinsa bisa ka’ida game da batun Taiwan, inda ya jaddada aniyarsa ta yin kokarin sake hadewa da yankin cikin lumana bisa gaskiya da himma, amma idan ’yan aware masu neman ‘yancin kan Taiwan suka tunzura jama’a, ko suka zarce layin da aka shata, tilas ne a dauki tsauraran matakai.

Sanin kowa ne cewa, babban yankin kasar Sin, ya amince da jagoranci da himma a dangantakar dake tsakaninsa da zirin Taiwan, kuma batun sake hadewar kasar Sin, wani yanayi ne na tarihi da ba za a iya jurewa ba.

Don haka, kasar Sin tana jan kunnen bangaren Amurka da kada ya raina kudiri da karfin da jama’ar kasar Sin suke da shi, na kare ikon mallakar kasa da cikakkun yankanansu. Kuma duk wani mataki na kalubalantar manufar kasar Sin daya tak a duniya, da kokarin dakile kokarin sake dinkuwar kasar Sin baki daya, tabbas ba zai taba yin nasara ba. Don haka Amurka ta daina tsoma baki a harkokin cikin gidan Sin.

LABARAI MASU NASABA

An Bude Taron Sanin Makamar Aiki Na Cika Shekaru 80 Da Kafuwar MDD A Wuhan Na Kasar Sin

Kamfanin Gine-Gine Na CCECC Ya Fara Gina Wani Titin Mota Da Zai Rage Cunkoso A Birnin Abuja Na Tarayyar Najeriya

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

An Bude Taron Sanin Makamar Aiki Na Cika Shekaru 80 Da Kafuwar MDD A Wuhan Na Kasar Sin
Daga Birnin Sin

An Bude Taron Sanin Makamar Aiki Na Cika Shekaru 80 Da Kafuwar MDD A Wuhan Na Kasar Sin

October 18, 2025
Kamfanin Gine-Gine Na CCECC Ya Fara Gina Wani Titin Mota Da Zai Rage Cunkoso A Birnin Abuja Na Tarayyar Najeriya
Daga Birnin Sin

Kamfanin Gine-Gine Na CCECC Ya Fara Gina Wani Titin Mota Da Zai Rage Cunkoso A Birnin Abuja Na Tarayyar Najeriya

October 18, 2025
Masanin Ilimin Physics Chen Ning Yang Ya Rasu Yana Da Shekaru 103
Daga Birnin Sin

Masanin Ilimin Physics Chen Ning Yang Ya Rasu Yana Da Shekaru 103

October 18, 2025
Next Post
‘Yansanda Sun Cafke Ali Madakin Gini, Kan Zargin Amfani Da Bindiga A Yakin Zaben NNPP Na Kano

'Yansanda Sun Cafke Ali Madakin Gini, Kan Zargin Amfani Da Bindiga A Yakin Zaben NNPP Na Kano

LABARAI MASU NASABA

JTF Ta Kama Wani Da Ake Zargin Mai Safarar Miyagun Ƙwayoyi Ne Ga ‘Yan Bindiga A Jihar Kogi

JTF Ta Kama Wani Da Ake Zargin Mai Safarar Miyagun Ƙwayoyi Ne Ga ‘Yan Bindiga A Jihar Kogi

October 19, 2025
Abin Da Nijeriya Ke Bukata Kafin Samun Damar Zuwa Gasar Kofin Duniya

Abin Da Nijeriya Ke Bukata Kafin Samun Damar Zuwa Gasar Kofin Duniya

October 19, 2025
Yadda Ake Alkaki

Yadda Ake Alkaki

October 19, 2025
Kar Ki Yi Kuskuren Da Za Ki Yi Da Na Sani A Kai (1)

Kar Ki Yi Kuskuren Da Za Ki Yi Da Na Sani A Kai (2)

October 19, 2025
An Sanya Hannu Kan Yarjejiyar Zaman Lafiya A Gaza

An Sanya Hannu Kan Yarjejiyar Zaman Lafiya A Gaza

October 19, 2025
Nijar

Gwamnatin Nijar Ta Yaye Tsofaffin Mayaka 369 Da Aka Bai Wa Horon Sauya Tunani

October 19, 2025
Yadda Zargin Takardar Karatun Bogi Ta Tilasta Wa Minista Nnaji Murabus

‘Yan Siyasa 11 Da Suka Faɗa Dambarwar Takardar Shaidar Karatu Ta Bogi

October 19, 2025
gombe

Ɗaliban Jihar Gombe Sun Samu Ƙarin Kashi 100 Na Kuɗin Tallafin Karatu

October 18, 2025
Ɗaliban Fasaha Sun Ɓullo Da Dabarar Tsaro Ta Harkar Noma

Ɗaliban Fasaha Sun Ɓullo Da Dabarar Tsaro Ta Harkar Noma

October 18, 2025
An Bude Taron Sanin Makamar Aiki Na Cika Shekaru 80 Da Kafuwar MDD A Wuhan Na Kasar Sin

An Bude Taron Sanin Makamar Aiki Na Cika Shekaru 80 Da Kafuwar MDD A Wuhan Na Kasar Sin

October 18, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.