Bishiyar Kanya (Black Ebony), na kammala girmanta ce bayan ta gama rika, sannan tana shafe shekaru 100 kafin kammala girmanta baki-daya, haka nan tana kuma yin tsawon da ya kai kafa 50.
Har ila yau, idan za ka ci amfaninta, ba wai sai ka jira ta kai har tsawon sama da shekaru 50 zuwa shekaru 200 ba.
- Zanga-zangar Karin Kudin Wuta: Gwamnati Ta Shelanta Matakin Da Za Ta Dauka
- Wike Ya Ba Shugaban Ƙasar Sanigal Bassirou Faye Shaidar Zama Ɗan Ƙasa A Abuja
Bishiyar na daya daga cikin Bishiyoyi masu tsada a fadin duniya, haka kuma akasarin mutane; ba su san muhimmancin da bishiyar ke da shi ba, kazalika a jikin bishiyar ce ake samar da gawayin Kwal tare da kuma sarrafa bishiyar zuwa kamar yin Kujeru da Gado da sauransu.
Tarihin Bishiyar Kanya:
Tarihin Kanya ya samo asali ne daga wasu kasashen da suka yi fice a duniya wajen samun kyakkyawan dausayi, inda hakan ya sa ake iya shuka ta har ta kai munzalin zama babbar bishiyar da za a iya yin hada-hadar kasuwancinta a fadin duniya.
A yanzu haka, farashin ingantacciyar Kanya ta kai kimanin dala 8,500 na ko wace mita daya, haka nan sarrafa katakonta zuwa wasu kayan kade-kade na zamani na kaiwa dala 12,500 a kowace mita guda.
 Bugu da kari, sakamakon irin muhimmancin da take da shi, hakan yasa nau’ikanta na ci gaba da bacewa ko yin karanci a halin yanzu.
Abubuwa 10 Da Ya Kamata A Sani Game Da Bishiyar Kanya:
1-Tsawonta na kai wa daga mita 10 zuwa 15
2-Ta fi ko wace bishiya tsada a duniya
3-Ba a cika samun bishiyarta a halin yanzu a duniya ba
4- Ita ce bishiyar da ke girma a hankali a duk duniya
5-Tana yin rassa masu yawan gaske
6-Ita ce bishiyar da ta fi girma a duniya, wadda nauyinta ya kai kilogiram 30(68)
7-Farashinta na da matukar tsada
8-Dabbobi kamar Biri, Giwa, Jimina, Karkanda da sauransu na dogara a kan bishiyar, don samun abincin da za su ci.
9-Ana amfani da ganyenta wajen maganin zazzabin cizon Sauro. 10- Ana kuma maganin Tari da ganyen nata.