Kungiyar Dattawan Arewa ta lissafo abubuwa uku da za su faru ga jam’iyyar APC mai mulki da kuma dan takarar shugaban kasa na APC Bola Tinubu bisa ga rungumar tsarin takarar Musulmi biyu a zaben 2023.
A jiya Lahadi ne dai, Tinubu ya shelanta cewa, ya zabo tsohon gwamnan jihar Borno, Sanata Kashim Shettima a matsayin wanda zai yi masa mataimaki.
- Hatsarin Jirgin Ruwa: Fasinjoji 15 Sun Mutu
- Dan Takarar Gwamnan LP A Osun Ya Tsallake Rijiya Da Baya Bisa Harin ‘Yan Bindiga A Gidansa
Amma Kungiyar ta bakin mai magana da yawunta, Dakta Hakeem Baba-Ahmed, ya bayyana cewa, Kiristocin kasar nan ba za su zabi APC a lokacin zaben na 2023.
Ya kara da da cewa, Musulmai ne kawai za su zabi Bola Tinubu.
Hakeem wanda ya sanar da hakan a shafinsa na Twitter, ya yi nuni da cewa daukar tsarin na Musulmai biyu ba zai nuna wani banbanci ba a makomar siyasar Bola ba.