Daruruwan masu ruwa da tsaki a jam’iyyar APC a jihar Legas sun gudanar da zanga-zangar lumana a kan wasu titunan da ke a jihar, inda suka nuna bara’a a kan bin tsarin takarar Musulmai biyu da APC ta bullo da shi don tunkarar zaben shugaban kasa a 2023.
Zanga-zangar wacce ta gudana a jiya Litinin, an yi ta ne a karkashin inuwar hadakar masu ruwa da tsaki na APC da kuma magoya bayan APC da suka fito daga Kudu maso Gabas.
- Sin: Cinikin Kayayyakin Abinci Zai Kara Amfanawa Jama’ar Sin Da Afirka
- Yawan Kayayyakin Masana’antu Na Kasar Sin Ya Karu Da Kaso 3.5 Cikin Watanni Bakwai Na Farko
Sun yi tattaki daga babban shagon Shoprite da ke a yankin Ikeja zuwa Majalisar Dokoki ta jihar da ke yankin Alausa, inda suke yin wake-waken tare da dauke da kwalayen da suka yi rubuce-rubucen cewa, Asiwaju ka sauya sunan Shettima a matsayin mataimakinka, ya kamata shugaba Buhari da Tinubu su sake yin tunani a kan tsarin takarar Musulmai biyu.
A jawabin da ya yi wa manema labarai a yayin zanga-zangar mai magana da yawun masu zanga-zangar, Samuel Arokoyo, ya sanar da cewa, matsalar da kawai APC za ta fuskanta a zaben 2023 shi ne yadda Tinubu ya dauko Shettima a matsayin mataimakinsa.
Arokoyo, ya nanata cewa amma inda Tinubu ya dauko dan Arewa kirista a matsayin mataimakinsa, zai iya samun kuri’un Kiritoci kashi 70 a cikin dari musamman daga jihohin Kogi, Kwara, Filato, Nasarawa, Benue, Taraba, Kaduna, Adamawa, Gombe, Borno, da Abuja
Wannan zanga-zangar dai ta biyo bayan makamanciyar wacce aka yi a yau wata daya sakakatariyar APC ta kasa da ke Abuja, inda masu zanga-zangar suka nuna bacin ransu kan tsarin na ‘yan takara Musulmai biyu.
Har ila yau, an kuma gudanar da makamanciyar irin wannan zanga-zangar a yayin da shugabanin APC na kasa suka kaddamar da Kashim Shettima a matsayin mataimakin Tinubu a dakin taro na Shehu Musa Yar’Adua da ke Abuja, inda masu zanga-zangar suka bukaci a sauya sunan Shettima da wani dan takara Kirista.