Yawan takardun Naira da ke hannun ‘yan Nijeriya ya kai tiriliyan 4.8 a watan Nuwamban 2024 duk da ƙarancin kuɗi da ake fama da shi a ƙasar.
Rahoton Babban Bankin Nijeriya (CBN), ya nuna cewa adadin ya ƙaru da kashi 7 cikin 100 idan aka kwatanta da watan Oktoban 2024, inda ya tashi daga tiriliyan 4.2 zuwa tiriliyan 4.6.
A 2024 kaɗai, yawan takardun kuɗin da ke hannun jama’a ya ƙaru da sama da tiriliyan 1, daga Naira tiriliyan 3.6 zuwa yanzu tiriliyan 4.8.
Duk da haka, ƙarancin kuɗi ya sanya bankuna ƙayyade yawan kuɗin da mutane za su iya cirewa a na’urorin ATM.
Wannan lamari ya jefa mutane da dama cikin ƙalubale wajen samun kuɗin da za su yi amfani da shi a rayuwarsu ta yau da kullum.