Jama’a, in kun yi la’akari da takardun kudi na kasa da kasa, za ku gano da cewa, hotunan da aka buga a takardun kudi na wasu kasashen Afirka, da ma sauran wasu kasashe masu tasowa, suna da alaka da kasar Sin.
Zanenmu na yau ya kuma nuna wasu abubuwan da aka buga a takardun kudi na kasashen Aljeriya, da Sudan, da Madagarscar da Malawi, wadanda suke da alaka da kasar Sin.
In mun dauki takardun kudi na Aljeriya ga misali, za mu ga cewa, an buga hoton babban masallacin kasar da aka sanyawa sunan Djamaa el Djazaïr, a takardun kudin kasar mai darajar Dinar 1000, masallacin da ma’aikatan kasar Sin suka shafe tsawon shekaru shida suna ginawa, bayan daidaita wahalhalu da dama da suka fuskanta.
An kaddamar da masallacin ne a shekarar 2017, wanda ke iya daukar musulmi kimanin dubu 36 a lokaci guda, wanda kuma ya kasance babban masallaci mafi girma na farko a nahiyar Afirka, kuma na uku a duniya baki daya.
Sai kuma a takardun kudin kasar masu darajar Dinar 500, inda aka buga hoton tauraron dan Adam na sadarwa na farko a kansa, tauraron da ya kasance irinsa na farko a kasar, wanda kasar Sin ta yi nazarinsa tare da harba shi a shekarar 2017, wanda ya taimaka wajen daidaita matsalolin sadarwa da suka shafi rediyo, da talabijin da yanar gizo, da samar da ilmi da sauransu a kasar.
Baya ga haka, a kasar Sudan, madatsar ruwa ta Upper Atbara da kamfanin kasar Sin ya dauki nauyin ginawa, ta taka muhimmiyar rawa wajen daidaita matsalolin samar da wutar lantarki, da ruwan sha, da kuma ban ruwa ga miliyoyin al’ummar kasar, wadda kuma ta samar da gudummawar bunkasa tattalin arziki da zaman rayuwar al’umma na kasar.
Sai kuma a Madagarscar, fasahar inganta irin shinkafa da masanan ilmin noma na kasar Sin suka samar ta sa yawan shinkafar da aka samar a kasar ta karu da yawan gaske, matakin da ya daidaita matsalar abinci ga al’ummar kasar da ke yawan dogara ga shinkafa. Domin bayyana godiyarsu, kasashen biyu sun buga hotunansu a takardun kudin su.
Hakika, irin wadannan labarai ba sa lisaftuwa. Cikin shekaru 10 da suka wuce, bisa ga shawarar Ziri Daya da Hanya Daya, an aiwatar da shirye-shiryen gina gadoji, da tashoshin jiragen ruwa, da hanyoyin mota, da layukan dogo, da tashoshin samar da wuta, da filayen wasa da dai sauransu da dama a kasashen Afirka da ma sauran kasashe masu tasowa, wadanda suka ba da babbar gudummawa ga bunkasuwar kasashen, da ma rayuwar al’ummominsu.
A yayin da kasar Sin ta samu gaggarumin ci gaban tattalin arziki da zaman al’umma, ta kuma yi kokarin raba nasarorinta ga sauran kasashen duniya, kasancewarta tana rungumar makomar dan Adam ta bai daya.
Kwanan nan, an bude babban taron wakilan jam’iyyar kwaminis da ke kan karagar mulki a kasar Sin ko (JKS) karo na 20, kuma a rahoton da ya gabatar wajen taron, babban sakataren kwamitin kolin jam’iyyar mista Xi Jinping ya yi nuni da cewa, kasar Sin za ta karfafa hadin gwiwa da kasashe masu tasowa bisa sahihanci da gaskiya, don kiyaye moriyarsu ta bai daya. A sa’i daya, kasar ta kuma, yi kira ga kasashen duniya da su yayata manufar kishin zaman lafiya, da ci gaba, da adalci, da dimokuradiyya da ‘yanci, don al’ummomin kasashe daban daban su kara kishin juna, su kuma martaba mabambantan wayewar kan duniya, su kara yin mu’amala da juna ta fannin al’adu, ta yadda za su kawar da sabani da rikice-rikice da suke fuskanta.
Zaman duniya, cude-ni-in-cude-ka ne. A ganin kasar Sin, da ci gaban duniya baki daya za a tabbatar da ganin ci gabanta, kuma ci gaban kasar zai taimaka ga tabbatar da karin ci gaban duniya.
Al’ummar kasar Sin na son hada hannu da takwarorinsu na duniya, don rungumar kyakkyawar makomar dan Adam ta bai daya. (Mai zane:Mustapha Bulama)