Abokai, ran 6 ga wata, an yi mummunar girgizar kasa a kudancin kasar Turkiyya dake dab da iyakar kasar Sham. Hukumar kiwon lafiya da dai sauran hukumomin ba da agaji na kasar sun ba da labari a ran 8 ga wata cewa, mutane a kalla 2500 sun mutu yayin da wasu 4000 suka jikkata a sakamakon bala’in.
“Muna matukar bukatar tallafi……”, bala’in ya rushe gidajensu, mutane da dama na karkashin buraguzai, ba a san ko suna da rai ko a’a ba, ana matukar bukatar agaji. Amma, sakamakon takunkumin da Amurka da dai sauran kasashen yamma suka dade suna kakabawa kasar, ana fuskantar karancin manyan na’urorin aikin ceto a kasar ta Syria, lamarin da ya sa wadanda suka tsira da ransu a bala’in suna hako ‘yan uwansu ta amfani da hannu kawai. Abu ne mai matukar bakanta rai, ganin yadda jama’ar kasar suke yin kuka suna zubar da jini, har ma wasu sun mutu bayan cetonsa saboda karancin jiyya!
Amma Amurka ta yi kamar ba ta ji ba ta gani, to ko mene ne ma’anar abin da take kira na kare hakkin Bil Adama, kuma me ya sa ba ta yi watsi da hukuncin da ta sanya wa kasar? Wadannan mutane da bala’in ya ritsa da su ba su da isashen lokacin jira, bala’u ba za a iya guje musu ba, amma mu Bil Adama na iya zabar taimakon ‘yan uwanmu. (Mai zana da rubuta: MINA)