Shahararriyar mawakiyar Afrobeats a Nijeriya Tiwa Sabage ta yi ikirarin cewa talauci ne ya jawo ake samun dimbin sabbin mawaka da masu harkar wasan barkwanci a Nijeriya saboda kasar ta yi wuyar zama hakan ya sa kowa ke fafutukar neman abinda ya ci ta hanyar nuna baiwarshi ta hanyoyi daban daban musamman waka.
A cewarta, wahalhalun da ake fama da su a kasar ya sa matasa suke auna basirarsu, da take magana wani shirin talabijin mai taken ‘Shopping The Sneakers’, Sabage ta ce zama a Nijeriya ya na da wahala.
- Abin Da Ya Sa Nake Rungumar Ɗana Ina Wakar Soyayya – Tsohuwar Matar Adam Zango, Amina
- Soyayya Ce Ta Yi Sanadin Fara Wakata – Princess Dabo
Ta ce, idan ka zo Nijeriya za ka fahimci dalilin da ya sa muke samun sabbin taurari da yawa, domin ka tsira a Nijeriya dole ka na bukatar wani abu da zai dinga samar maka yan canji, saboda haka kowa yake buga buga domin a samu abinda za a dinga kaiwa bakin salati inji ta, dole mawaka su yi yawa don kowa ya na ganin yana da basirar waka kuma ana samun kudi a harkar.
Nijeriya ita ke da manyan masana’antun fina-finai, kida,wasan kwaikwayo da masana’antar kayan kwalliya a nahiyar Afirka, Nollywood ita ce babbar masana’antar fina-finai ta biyu a duniya a bangaren yawan mutanen da suke cin abinci a cikinta.