Kungiyar ‘yan kasuwan mai masu zaman kanta (IPMAN), ta ce tallafin da ake kashewa a Nijeriya a bangaren mai ya zarce biliyan 700 duk wata.
- Za A Ci Gaba Da Fuskantar Karancin Man Fetur – IPMAN
- IPMAN Ta Yi Barazanar Rufe Gidajen Mai Sama Da 30,000 Saboda Bashi
Sakataren IPMAN, reshen Abuja-Suleja, Mohammed Shuaibu, shi ne ya shaida hakan a wata sanarwar manema labarai da ya fitar a ranar Litinin.
Yana maida martani ne kan bayanan da kungiyar ‘yan kasuwan makamashi a Nijeriya (MEMAN) suka fitar a ranar Laraba, ya lura kan cewa kudin saukar man fetur lita guda a wannan ranar ya kai naira 1,117.
Da yake magana kan bayanan kungiyar MEMAN, Shuaibu ya ce, da yiyuwar gwamnatin tarayya da kamfanin mai fetur na kasa ba za su fito su fadi gaskiya kan tallafin mai da kasar ke kashewa ba.
Sai ya gargadi ‘yan Nijeriya da cewa su fara zaman shirin fuskantar karin kudin mai fetur.
“Farashin mai fetur na dogara ne kan karfin yawan bukatarsa da kuma yanayin wadatuwarsa a kasuwannin duniya. Duk lokacin da farashin ya karu a kasuwannin duniya, dole a Nijeriya ma ya shafemu.
“Don haka mu zauna da shirin fuskantar karin farashin mai a kowani lokaci, ka da mu sha mamaki domin tuni sun fada mana,” Shuaibu ya shaida.
Sai dai kuma, a wurare daban-daban, karamin ministan albarkatun mai fetur, Heineken Lokpobiri, ya sha nanata cewa an jima da cire tallafin man fetur a Nijeriya.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da aka fara samun takun tsaka tsakanin matatar man kamfanin Dangote da hukumar kula da samar da mai ta kasa kan batun ingancin albarkatun mai.
Idan za a tuna dai, a kwanakin baya tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir el-Rufai, ya yi ikirarin cewa gwamnatin Bola Tinibu tana biyan tallafin mai fiye ma abun da ake biya a baya.