A halin yanzu a duk fadin kasar Sin, ana samun wani irin sabon sauyi kan abin da ya shafi kyautata walwalar rayuwar yau da kullum ta miliyoyin jama’a, inda gwamnatocin manyan birane ke bude hanyoyin kashe kudi da ciniki a bangaren gidajen cin abinci, da yawon bude ido, da wasannin motsa jiki da kuma harkokin nishadi.
Daga irin kamshin dake tashi a gidajen cin abinci na birnin Zhengzhou zuwa sowar masu sha’awar kwallon kwando a Zhejiang, za a fahimci irin yadda mahukuntan biranen suke bullo da shirye-shiryen bayar da tallafin kashe kudi domin kara kuzarin ruhin walwalar al’umma.
A Guangzhou, ana bai wa masu sha’awar zuwa gidajen cin abinci wata kyakkyawar dama bisa yadda ake raba musu takardun tallafin cin abinci. A karkashin wannan tsari a zagaye na biyar, daga watan Disambar bara zuwa yanzu an raba takardun tallafin adadin yuan miliyan 100 wadda mutane suka yi amfani da su wajen ciye-ciye da tande-tande. Mahukuntan lardin Zhejiang sun fahimci yadda haduwar mutane a wuraren cin abinci ke inganta walwalarsu da kuma kara dankon soyayya da zumunci a tsakaninsu, kana da samar da karin karfi ga tattalin arziki.
Lardin Hubei shi ma ya bi sawu, inda ya bullo da nasa shirye-shiryen na raba takardun tallafin tare da mai da hankali musamman a kan bangaren da ya shafi cin abinci. Babban makasudin hakan shi ne a karfafa mutane su rika fita zuwa gidajen cin abinci. Wannan ya kara farfado da salon cin abinci tare a tsakanin Sinawa da kuma kwarya-kwaryan harkokin da ake yi a gefen wasu tituna bisa tsari. Baya ga bunkasa tattalin arziki, wannan dabara tana samar da yanayi mai dadi da faranta ran jama’a.
Shi ma birnin Shanghai ba a bar shi a baya ba a kan wannan sabga, inda shi kuma ya mayar da hankali a kan nishadantarwa ta fuskar al’adu. Birnin ya ware makudan kudi yuan miliyan 500 domin karfafa zuwan jama’a wurare da dandaloli na wasannin kwaiwakyo, da wasannin ban dariya, da harkokin wasanni na zamani da sauransu, inda a zagayen farko aka fara kashe yuan miliyan 30. A karkashin wannan tsarin na tallafi, mutane sun kashe fiye da yuan miliyan 91 a bangaren wasanni a birnin na Shanghai.
Shi kuwa lardin Zhejiang ya zo da wani salo ne na musamman mai hangen nesa, inda ya hade wasanni da yawon bude ido a bangaren karfafa walwalar jama’a da kashe kudi. Masu sha’awar kwallon kwando suna amfani da tikitin wasanni mai rangwame da lardin yake bayarwa don garzayawa wuraren wasanni masu jan hankali, da gidajen abinci da sauransu. Yin hakan wata fasaha ce ta karfafa hanyoyin taimakawa ci gaban tattalin arzikin cikin gida ta fuskar tsarin gudanar da rayuwar jama’a.
A can birnin Guangzhou ma, sama da mazauna birnin miliyan 6 ne suka yi amfani da takardun tallafin cin abinci, inda aka kashe yuan miliyan 409. Hakika wannan yana nuna cewa, duk lokacin da aka buda wa mutane sararin shiga a dama da su, to za su yi hakan da zuciya daya kuma cikin jin dadi.
A kwanan nan, wasu mahukunta a kasar Sin sun jaddada bukatar kara fadada hanyoyin cin gajiyar harkokin rayuwa na yau da kullum da ake kashe kudi wajen gudanar da su, don haka wadannan dabaru da gwamnatocin biranen suka bullo da su, suna ba su damar jifan tsuntsu biyu da dutse daya, ga amfanin da za a samu ta fuskar karuwar tattalin arziki musamman ga kananan masu sana’o’i, ga kuma inganta jin dadi da walwalar jama’a. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp