Kama tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato, Sanata Aminu Tambuwal, da Hukumar EFCC ta yi ya jawo ce-ce-ku-ce a shafukan sada zumunta.
Hukumar ta riƙe Tambuwal daga Litinin har zuwa yammacin Talata bayan ya amsa gayyatar EFCC kan zargin almundahanar kuɗi Naira biliyan 189 lokacin da yake gwamna.
- ‘Yansanda Sun Fara Bincike Kan Rasuwar Wani Dan NYSC A Bauchi
- EFCC Ta Bayar Da Belin Tambuwal, Ta Yi Allah-wadai Da Zargin Da Jam’iyar ADC Ta Yi
Jam’iyyarsa ADC da wasu abokan siyasarsa sun zargi EFCC da nuna son kai wajen yaƙi da cin hanci, inda suka bayyana cewa hukumar na mayar da hankali ne kan ’yan hamayya tana barin mambobin jam’iyyar da ke mulki.
Sai dai EFCC ta ƙaryata wannan zargi, tana mai cewa tana bincikar dukkanin’yan siyasa daga kowanne jam’iyyu.
Ta kuma ce maganganun ADC ta yi ba gaskiya ba ne.
Shugaban EFCC, Ola Olukoyede, ya ce, “Idan ba a zarge ni wajen binciken gwamnoni da ministocin jam’iyyar da ke mulki ba, bai kamata a zarge ni idan na binciki ’yan hamayya ba.”
Duk da haka, mutane da dama a kafafen sada zumunta sun nuna shakku, tare da tambayar dalilin da ya sa EFCC ba ta ɗauki mataki kan manyan ’yan siyasa na jam’iyyar APC kamar tsohon Gwamnan Delta Ifeanyi Okowa, tsohon Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje, da tsohon Gwamnan Kogi Yahaya Bello ba.
Wasu sun zargi EFCC da yin aiki ƙarƙashin ikon gwamnatin da ke mulki, yayin da wasu suka yi tsokaci ta hanyar buƙtar shugaban EFCC ya bayyana bayanan asusun bankinsa na yanzu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp