Hukumar Shirya Jarrabawar Shiga makarantun gaba da sakandire (JAMB) ta fitar da sakamakon jarrabawar shiga jami’a (UTME 2025) da aka sake yi wa Ɗaliban da aka samu tangarɗar na’ura a yayin tattara sakamakon jarabawar da suka yi a farko.
Hukumar ta bayyana hakan ne a shafinta na X (Twitter), a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a na hukumar, Dr. Fabian Benjamin.
Hukumar JAMB na nuna godiyarta ga Hukumar shirya jarabawar kammala sakandire ta Afrika ta Yamma (WAEC) bisa yadda ta samar da kofar sake jarabawar da aka samu tangardar na’ura yayin tattara sakamakon Ɗaliban da abin ya shafa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp