Assalamu alaikum, Barka da kasancewa cikin wannan shafi me albarka. Tofic dinmu na mako zai duba ne ga BAMBANCIN TARBIYAR YANZU DA TA DA saboda muhimmancisa ga al’umma musamman wannan zamanin da sai dai mu ce Alhamdu lillah. Inda na sama tattaunawa da wasu daga cikin iyaye ta hanyar musu tambayoyi da suka shafi TARBIYAR ‘ya’yayenmu wadanda suka kasance Amana gare mu. Kafin mu kai ga kan tambayoyi da amsoshi yana dakyau musan meye ita kanta TARBIYAR a Musulunci.
Manufar Tarbiya a Musulunci tana nufin ” Gina cikakken mutum sannu a hankali don bin umarnin Allah da Manzonsa, da kuma neman yardar Allah, da Samar masa nagartaciyyar Rayuwa duniya da lahira, a bisa tsari na Musulunci.” Wannan ita ce Manufarta a Musulunci. Tabbas! Rashin tarbiya kan kawo koma baya ga al’umma kafin na ci gaba da bayani ga Topic na Tambayoyi da na bai wa wasu daga cikin iyaye tare da amsoshin dana samu.
Tambayoyi
1. Shin a matsayinki na uwa me, me kika fuskanta game da yaran yanzu da na da?
2. In akwai banbanci da matsala a ra’ayinki wace hanya ce masalaha?
3. Abu na karshe in kika yi duba Allah ya kawo mu zamani inda za ki ga yara masu karancin shekaru da Wayoyin Hannu manya. Shin me za ki ce game da hakan kina ganin ya dace a ba yaro masu karancin shekaru waya? Meye amfaninta gare su tare da illar hakan?
Amsoshi
Hajia Binta Balarabe: Assalamu Alaikum barkanmu da wannan lokaci zan yi dan bayani ne a kan yaron da da na yanzu magana ta gaskiya a matsayina na uwa da na ga jiya kuma yau ma ga mu a cikinta, akwai bambanci a kan yaran da da na yanzu.
Yaro a da idan ka yi mishi magana ko ba fada bare doke-doke zai ji zai gane.
Wani lokacin cikin dabara za ki nuna masa rashin dacewar abu zai kiyaye shi. Amma yanzu idan ka ce wa yaro ka za ba kyau ka dena ko kar ka yi burinsa ya yi ya ga abun da kake fada haka ne?
Sai dai yaron yanzu suna da kaifin basiri tun suna yara wayonsu ya fi shekarunsu kin ga kuwa dole a sami bambanci a tarbiyyarsu.
Yaron da suna da saukin ma’amala da wahala ki ga a makaranta ya fi karfin malami amma ban da yanzu wani lokacin sai an hada da iyayen yaro. Sai dai Allah ya ba mu ikon tarbiyantar da yaranmu.