An haifi Hassan Usman Katsina ne a ranar 31, ga watan Maris shekarar 1933. Da ne ga mahaifinsa Sarkin Katsina Sir Usman Nagogo tare da abokin haihuwarsa Hussaini da ake kiransa da sunan (Naini). Sunan mahaifiyarsu Fatima, sai dai an fi kiran ta da sunan Cima ko Hajiya Uwargida ‘yar Wazirin Katsina, Haruna ce.
Hassan Usman Katsina bai kai shekara shida ba lokacin da aka kai shi gidan Kankiya Nuhu wanda shi Kaka ne a wurinsa domin kuwa kanen Sarkin Katsina Muhammdu Dikko. Kamar dai yadda aka saba a kasar Hausa lokacin da ayake tasowa ne aka kai shi makarantar Islamiyya ya yi karatun Allo. Daga shekarar 1940- 1944 ya yi makarantar Elemantare ta Kankiya daga can kuma sai ya wuce zuwa, makarantar Midil ta Katsina daga 1944-1947. Bugu da kari Hassan Usman Katsina ya halarci Kwalejin Barewa ta Zariya, daga 1948-1951.Daganan kuma sai makarantar koyon harkokin mulki ta Zariya a 1952, daganan kuma sai ya halarci Kwalejin Kimiyya da fasaha ta Njeriya da ke Zariya a 1953-1955.
- Wasu Daga Cikin Muhimman Alamomin Ciwon Kansa
- Barin PDP Zuwa Wata Jam’iyyar Alamun Rashin Jarumta Ne – Gwamnan Bauchi
Kamar yadda abin ya kasance sai Hassan ya bada labarin “Watarana na zo wucewa zuwa wurin cin abinci sai na ga an manna takarda ta neman ‘yan Arewa wadanda suke sha’awar zuwa aikin soja. Sai na ce ina so; ni dai kawai na ji ina so ba da wani na yi shawara ba, na yi kokarin bin ka’idar shigar ne. Amma ban fada ba, don ba na son tsohuwata ta ji. Idan ta ji ba za ta yarda ba. Da aka yi hutu na koma gida sai na sanarwa mahaifina Sarkin Katsina Usman Nagogo, cewa ina sa ran takarda ta neman tafiyar makarantar horar da hafsoshin soja. Sai ya ce, ka fada wa Hajiya?’ Na ce ‘a’a ban fada mata ba’, Sai ya ce to kar ka fada mata”.
Ya ci gaba da bayanin cewa, “Da zan koma Kaduna sai ya ba ni takarda na kai wa Wazirin Katsina, Alhaji Isa Kaita. Na zo Kaduna na yi jarrabawa, bayan mun kare na koma gida ina sauraren sakamakon jarrabawar. Ba zan taba mantawa ba, ana zaune wajen Hawan Daba don tarbar Sarauniyar Ingila sai na sami telegiram mai cewa na ci jarrabawa ana nema na a Kaduna.
“Na fadawa mahaifina. Muka kintsa muka bar Katsina sai Kaduna, daga Kaduna muka tafi Legas. Da isa ta Legas sai na ga abokan nawa da suka sami nasarar wannan tafiyar duk ‘yan Kudu ne. Ni kadai ne dan Arewa kuma Bahaushe cikin daga cikin mu takwas