Shi dai sunansa na gaskiya Amjad Zakaria Khan ana yi masa lakabi da (Gabbar Singh) ya sami wannan sunan ne acikin film din (Sholay) 1975. kamar yanda kuka sani Amjad Khan ya yi fice ne a bangaren fitowa a matsayin mara tausayi da imani kamar yadda muka gani a film dinsa na Sholay, baya da haka Amjad Khan ba a iya jarumi bane a masana’antar ta Bollywood ya kasance me ba da umarni ne a kan fina-finan indiya masana kimiyyar sanin dan’Adam sun tabbatar da kalar idon Amjad inda suka ce ya kasance ruwan kasa ne me duhu. Haka zalika kalar idonsa baki ne.
Amjad Khan An haife shi ne a ranar sha-biyu 12 gawatan (Nobember) a cikin shekarar (1940), cikin garin da aka haife shi shi ne Feshawar, British India wanda a yanzu yana Fakistan).
- Shugabar Kasar Honduras Ta Fara Ziyara a Kasar Sin
- Hukumar GEIDCO Ta Zayyana Ayyuka Da Za A Samar A Afirka
Bisa binciken da muka yi mun gano cewa Amjad Khan ya mutu ne a ranar sha-bakwai 27 gawatan (july) na shekarar 1992, ya mutune a cikin garin Mumbai indiya.
Daga lokacin da aka haife shi 1940 duwa shekarar da ya mutu 1992 jimillar jadawalan shekarunsa sun kama shekararsa (51). Kafin jarumin ya mutu yana zaune ne a garinsa na haihuwa wato Mumbai indiya,
Mun yi duba na tsanaki tare da nazari wajen bincikar abin da ya haddasa mutuwarsa, yandu mun samu gamsassiyar hujja kan abin da ya yi silar raba shi da duniya.
Wani gidan jarida me zaman kansa a kasar indiya ya tabbatarwa da duniya cewa, ciwon zuciya shi ne ya yi sanadiyyar mutuwarsa bayan hatsarin mota da ya yi kamar yadda wannan kafa ta wallafa labari akan hakan.
Baya da haka Amjad Khan ya yi wata makaranta me suna school st. andrew’s high school, bandra, bombay.wacce take garin Mumbai….ya dora da karatunsa a cikin wata kwaleji wacce ake wa lakabi da R.D. National College, Mumbai.A yandu haka yana da shedar takardar kammala karatunsa afannin (Fhilosofhy)
Jarumi Amjad Khan tun yana yaro ya fara fitowa a film ya fito ne a cikin wani film mai suna Nazneen an yi shi ne a (1951).
Fim din da aka fara ganinsa a matsayin jarumi wanda yake jagorantar fim shi ne Hindustan Ki Kasam wanda a kai a (1973), Hakazalika ya fara fitowa ne a mataimakin mai ba da umarni a wani film me suna Lobe and God da aka yi shi a 1963 kuma aka sake shi a shekarar 1986), baya da haka ya fara ba da umarni ne tun a 1983 acikin wani fim wanda ake masa lakabi da Chor Police. Jarumi Amjad Khan akwai wani karin magana da ya fiye yi a cikin finafinansa irinsu
kitne aadmi ?Ab tera kya hoga kalia,Holi kab hai, kab hai holijo dar gaya, samjo mar gaya yeh haath hum ko de de, thakur.
Wadannan su ne irin karin maganar da ya fiya yi a cikin fina-finansa wanda suka gabata a baya, an samu rahoto daga wata majiya akan sunayen danginsa to da farko sunan mahaifinsa Jayant Aka Zakaria Khan wanda shima ya kasance fasihin jarumi ne a masana’antar ta Bollywood, baya ga haka, sannan yana da ‘yan uwa maza daga ciki akwai Imtiaz Khan da Inayat Khan.
addinin Musulunci shi ne addinin da jarumin ya yi imani da shi, bisa binciken da kimiyyar tamu ta yi mun gano cewa jarumi Amjad Khan akwai abubuwanda suke burge shi a rayuwarsa kafin ya mutu ya bayyanawa manema labarai cewa daga cikin abubuwanda suka fi burge shi a rayuwarsa da farko akwai tukin mota.da sauraron wakokin gargajiyar su.
Sannan ya kara da cewa mawakin da ya fi burge shi shi ne shahararrun mawaka @n nan wadanda sukai fice wajen sarrafa sautin waka dama wakar kanta wato r. d. Burman & kishior kumar.
A bangaren jarumai kuwa jaruman da suka fi burge shi da shiga cikin zuciarsa su ne manyan mashahuran jaruman nan wato Amitabh Bachchan da Amrish furi, a jarumai mata ma ya bayyanwa duniya cewa jarumar da ta fi burge shi ita ce.. Madhubala.
Amjad Khan ya yi aure ne tun a ranar 17 ga watan (Yuli) a cikin shekarar 1972, sunan matar da ya aura Shehla Khan, hakazalika Allah ya azurta su da yaya guda 3 biyu daga ciki maza ne sai mace guda daya, sunansu.. Shadaab Khan, Seemab Khan da Ahlam khan.
Amjad Khan ya samu nasarori na zamowa zakaran gwajin dafi duk da cewa bai dade yana fim ba Allah ya karbi rayuwarsa daga cikin nasarorin kambunan kyautittikan da ya samu akawai.
kyautar filmfare (1986) kyautar jarumin da ya fi kowa ban dariya
Sai kuma lashe kyautar jarumin da ya fi iya taimakawa jarumi a (1982)
Ya sake lashe kyautar jarumin da ya fi iya taimakawa jarumi a (1982)
Ya sake lashe kyautar jarumin da ya fi iya taimakawa jarumi a (1980)
Ya sake lashe kyautar jarumin da ya fi iya taimakawa jarumi a (1985)
Ya sake lashe kyautar Yaarana a (1981) da kuma (1979).