Bayanin baka ya nuna cewar Tera na daya daga cikin masu neman sarautar Ngazargamu a tsohuwar daular Borno kuma su suke sarautar a jamhuriyar Nijar wanda har yanzu suna da kyakkyawar alaka da junansu.
Wasu daga cikin jama’ar Kanuri da suke zaune a Geidam wanda a halin yanzu take cikin jihar Yobe sun guje wa jihadin Rabeh a cikin shekara ta 1890, wanda ya kai su ga gangarowa ya zuwa Gwara wadda aka fi sani da Gora.Wannan gari na kusa da garin Shani a cikin kasar Borno.
- Wata Kungiya Ta Shirya Samar Da Gidaje Masu Saukin Kudi 400,000 A Nijeriya
- Jihar Benuwai Ta Bankado Mutum 35 Masu Yi Wa Sirin Tattara Harajinta Zagon-Kasa
Auratayya da kabilar Kanakuru kuma a dalilin haka suka samar da kabilar Komberi, ita ma wannan kabilar ta jirga ya zuwa gundumar Tera.Yake-yaken jihadi sun ci gaba kuma jama’a sun ci gaba da hijira daga wannan wuri zuwa wancan wuri har ya zuwa shekara ta 1808 inda Fulani suka kama yammacin Ngazargamu wanda yake shi ne birnin daular Borno. Amma daga karshe a cikin shekara ta 1809 Sheikh Lamido ya kori Fulani daga daular Borno.
Wannan kai-komo ya sa Rabe ya rasa wajen zama inda ya bar Zindar ya tafi ya zuwa gabashin Nijar a cikin shekara ta 1893. Wannan ya zo daidai da Turawan Faransa sun shigo kasar Nijar kuma suka kashe shi a wani gari mai suna Kousseri cikin kasar Kamaru a shekara ta 1900.Hakan lamarin ya faru ga dansa da shi wanda aka kashe shi a wani gari mai suna Gujba ta hanyar yaudara wanda Turawan Faransa su kai masa a shekara ta 1901.A can ne kuma Turawan Faransa suka hadu da Turawan Ingila kuma turawan Ingila suka nuna wa Turawan Faransa cewar sun wuce iyaka kasar Faransa, wanda a yanzu suna cikin kasar da ake kira Nijeriya.Hakan ta faru a inda Faransawa suka ba Turawan Ingila wuri.
Masallacin fada
Sarki Makau
Dangane da rayuwar kasar Zazzau kuwa, Sarkin Zazzau Muhammadu Makau ya samar wa ‘yan-uwansa wurin zama ba tare da sun tsoma kansu cikin rikicin mulki da wasu suka haramta masu don bukatar mulkar kasarsu ba.Zazzagawan asali,sun mai da martani ga sabuwar masarautar Zazzau a inda suka tare mashigin dake tsakanin kudancin kasar zuwa kasar Zazzau domin tauye kasuwancin da ke tsakaninsu da jama’an kudancin kasar nan.Hakan nan ma sun taimaka wa Turawa wajen cin kasar Zazzau,domin daidai da wannan lokaci ne Turawa suka bullo.Zazzagawa sun taka babbar rawa wajen cin kasar Zazzau a wancan lokacin. A cikin rubuce rucen Hausa Fulani sun so karin yin bayanan ga jama’ar Zazzau ta dauri musamman a kan yadda ta kasance da Sarkin Zazzau Muhammadu Makau ta wajen neman kau da gaskiyar al’amurra. Kuma sun hada gabas da yamma wuri guda.Watau wajen dauko tarihi Barebari suka gauraya a cikin tarihin Zazzau ta dauri.Inda suka dauko tarihin Albarka wanda yake shi dan Sarkin Kukawa ne can cikin kasar Borno kuma ya zo kasar Zazzau a sanadiyyar rikicin Sarauta.Albarka bai da niyar zama kasar Zazzau sai dai ya yada zango ya wuce.Wannan ya faru ne a zamanin Sarkin Zazzau Alu Dan Sidi. Amma ga al’amarin Sarki sai ya jawo hankalinsa da ya zauna a nan kasar Zazzau.Sarki ya yi masa alkawarin bashi duk bakin inda ya yi jifa ta tsaya kyauta.Hakan kuma ta faru,wannan wuri ya kama tun daga bakin kotu ya yi iyaka da kwarin fadama.A dalilin haka ne wannan wuri ya samu sunansa (Albarkawa).Malam Usman Katuka Sabulu da ne ga Sarkin Kano Al-wali kuma jika ne a gidan Sarautar Zazzagawan dauri (Zazzau),inda Sarki Isyaku Jatau ya dauki ‘yar kaninsa Malam Muhammadu Megamo ya ba da aurenta ga Sarkin Kano Al-wali.Usman Katuka Sabulu ya zo kasar Zazzau wajen kakanninsa don koyon karatu da samun ilmin addinin Muslinci, kuma Allah ya nufa wajen arzikinsa ke nan a dalilin goyan bayan da ya ba juyin mulkin Filato Barno da kuma Hausa Fulanin a kasar Zazzau,(domin suna kiran kansu a matsayin Fulani)a lokacin yi ma gidan kakanninsa bore don kaucewa halin da zai iya shiga bayan basu ko kuma a bisa wasu dalilai nasa.Daga karshe Sarkin Zazzau na farko a daular Hausa-Fulani a kasar Zazzau Malam Musa ya amince da Usman Sabulu kuma ya umurce shi da ya zauna a daya daga cikin gidajen kakanninsa watau na Zage zagi kuma aka ba shi sarautar katukan farko a daular Hausa Fulani.Katuka Usman ya samu tsawon Sarakuna biyu a daular Hausa Fulani kafin a tsige shi daga kan sarautar; wato Mu’sa dan Yamusa.