Babban tushe mafi mahimmanci ga farkon tarihin Zazzau shine tarihin da aka kirkira a farkon karni na 20 daga al’adun baya.Yana ba da kuma labarin gargajiya ne na kafuwar masarautun kasar Hausa daga jarumin al’adu Bayajidda,kuma ya ba da jerin sunayen masu mulki tare da tsawon lokacin da kuma suka yi sarauta.Dangane da wannan tarihin, an ce asalin masarautar hausa ko Habe ta fara ne tun daga karni na 11, wanda Sarki Gunguma ya kafa. (1) Wannan majiyar kuma ta sanya ta zama daya daga jihohin Bakwai.
Mafi shaharar sarautar Zazzau ita ce Sarauniya (ko kuma Gimbiya) Amina, wacce ta yi mulki ko dai a tsakiyar karni na 15 da tsakiyar na 16, kuma Muhammed Bello ne ya rike ta, masanin tarihin Hausa a karni na 19 kuma Sarkin Musulmi na biyu, shine farkon wanda ya kafa daula a tsakanin Hausawa(2).
Zazzau ta kasance wurin tattara bayi ne don a kai su zuwa kasuwannin Arewacin Kano da Katsina, inda ake musayar su da gishiri tare da ‘yan kasuwar da ke jigilar su zuwa Arewacin Sahara.(3) Dangane da tarihi a cikin littafin, an gabatar da addinin musulunci ga masarautar a wajen shekara ta 1456, amma ga alama ya bazu a hankali, kuma tsafin arna ya ci gaba har zuwa lokacin da Fulani suka ci shekara ta 1808.A wasu lokuta a tarihinta,Zazzau ta kasance tana karkashin kasashen makwabta irin su Songhai, Bornu da kuma Kwararafa.(4) Wannan karin rubutu da aka sa bai daidaitu ba domin a kwai tsallaken zance a dukkanin sakin layin. Zazzagawa an same su da addinin musulunci kuma Shehu Usmanu ya tabbatar da hakan.Tun asali kasar Zazzau ba su da maguzawa.
Masarautar Gidan Fulani
A watan Disamba na shekara ta 1808 babu Fulani a cikin wadanda Shehu Usmanu Danfodiyo ya turo su da su kifar da ko su fidda Sarkin Zazzau Muhammadu Awwal Makau daga kasar Zazzau, illah kinibibin da ya kullu a tsakanin Malaman da suke zaune a kasar Zazzau.Wannan ya biyo bayan hijirar da Sarkin Kano Muhammadu Al-wali ya yi bayan kashe shararren Malamin nan malam Dan Zabuwa wanda ya ke shima bafillace ne. Ganin haka Fulani su kai gangami wajen tuntsurar da mulkinsa. Sarkin Kano ya yi kaura zuwa kasar Zazzau,a lokacin mulkin Sarkin Zazzau Muhammadu Awwal Makau a cikin shekara ta 1807 amma bai samu hurumin zama ba. Duk da cewar shi suruki ne ya ke ga Sarkin Kano Muhammadu Al-wali.Wannan hijira ta Sarkin Kano
Muhammadu Al-wali ita ta kawo cece-kuce a kasar Zazzau inda a karke ya kawo karken mulkin Sarkin Zazzau Muhammadu Awwal Makau. Inda gaurayen kabilun Malaman da ke zaune a kasar suka hada kai suka kifar da mulkinsa bayan ya tafi masallacin Idi don gabatar da Karamar sallah .
Domin ta wannan dalilin ne ya sa shi tilasa ya bar kasar Zazzau inda ya kafa kasar Abuja kuma a halin yanzu ita ce aka kafa hedikwatar kasar nan.Kuma masarautar ta sauya da sunan sarki Sulaimanu Barau watau Suleja. Kalmar Fulani ta samu ne dalilin Shehu Usmanu.Amma malaman kabilun da ke zaune su ne: kabilar Mande a yau a na kiransu Mallawa,Barebari, Sullubawa da kuma Katsinawa.
Mun samo daga Wikipedia Hausa