• English
  • Business News
Saturday, July 12, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Tarihin Rayuwar Marigayi Sarkin Ibira, Ohoniyi Attah Ado Ibrahim

by Idris Aliyu Daudawa
2 years ago
in Tarihi
0
Tarihin Rayuwar Marigayi Sarkin Ibira, Ohoniyi Attah Ado Ibrahim
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

An haifi Abdulrahman Ado-Ibrahim ranar 7 ga Fabrairu 1929 shi ne Sarki na hudu na Sarautar gargajiya ta Ohinoyi ta Ebiraland mai hedikwata a Okene,Jihar Kogi na dan Attah na biyu ne yanzu “Ohinoyi”) na Ebiraland, Ibrahim Onoruoiza na gidan Sarautar Omadibi da ya yi mulki daga shekarar 1917 zuwa 1954.An nada Ado-Ibrahim a matsayin Ohinoyi na masarautar Ebira shekarar 1997 haka ya yi ta mulki har zuwa ranar lahari 29 Oktoba 2023 ya yi shekara 26 kafin rasuwar shi. Kafin a nada shi a mukamin Sarauta dan kasuwa ne wanda ya shahara wanda yawancin rayuwarsa ya zauna ne a Legas.Ado Ibrahim dan mai martaba,Alhaji Ibrahim Onoruoiza Attah da Hajiya Hauwawu Ozianuba.

Matashi Ado Ibrahim ya kammala makarantar gwaji data karatun Alkur’ani yana da shekara 11 years Daga na sai makaranatar Okene ta mulkin turawa daga shekarar 1934 zuwa 1940 saboda karunsa na Elimantare bayan ya kammla ta sai sai ya wuce zuwa Okenen.Bayan ya kamala a 0kene a 1941.Bayan yayi shekara biyu sai ya wuce shahararriyar makarantar Ondo Boys High School saboda ilimin Sakandare daga 1943 zuwa 1946.Daga 1947  – 1949 ,ya tafi kwalejin Oduduwa inda ya kammala karatun shi na Sakandare.

  • Ina Da Kwarewar Shugabancin Majalisa Fiye Da Akpabio – Ndume
  • Yadda Matata Ta Rasu A Kokarin Kare Mutuncinta Daga Masu Garkuwa – Yusuf

Kamfanin United African Company (UAC) ya dauke shi aiki a 1950 matsayin sabon shiga na irin aikin Shugabannin kamfanin, da ya samu kwarewa a bangaren al’amuran kudi da sayar da kaya a shekara ta 1952 sai aka kara ma shi girma aka mai da shi Kaduna a matsayin Manaja a Kamfanin Kingsway Stores, na Kaduna.

A Janairu 1953 sai ya ajiye aiki inda ya je Jos a matsayin Jami’i mai kula da harkokin ma’aikata a kamfanin Amalgamated Tin Mines na Njeriya a matsayin wanda ke sa ido akan yadda ayyuka suke tafiya a garuruwan Bukuru da Barkin Ladi.Duk a cikin shekarar ya yi makaranta ta farko data shafi al’amarin hakar ma’adinai a Jos inda hakan ne ya sa ya samu kwarewar da ta bashi damar samun mukamin Manaja.

A cikin shekarar sai Kamfanin ya tura shi kasar Afirka ta Kudu domin ya halarci wani kwas da ya shafi fasaha,wanda kamfaninin hadin gwiwa kan harkar ma’adinai.

Labarai Masu Nasaba

Yadda Cinikin Bayi Ya Fara A Nahiyar Afirka (1)

Tarihin Shugaannin Kasar Mali Na Farko A Daular Songhai (8)

Bayan ya dawo ne sai aka yi ma shi karin girma da mukamin Manajan sashe inda aka bas hi wani aiki dangane da tono ma’adinan Lead/Zinc Ore da suke a Izom a garin Hakimi na Abuja,da kuma jagoranta tawagar neman gwal da base a wurin.

Kafin ya kai ga samun karin matsayin ya yi rajista a matsayin dan makarantar da ba cikin makaranta yake ba domin karatun digiri a makarantar tattalin arziki ta Landan,ya kuma yi amfani ne da kayan da za su taimaka masa da kayan da aka samar a dakin karatu na na kulawar cibiyar karatu ta Ingila a Jos.

Ya hada aikin shi da ya shafi harkar ma’adinai da karatun da yake yi wanda har ya samu takardar digiri akan kididdiga daga makarantar tattalin arziki ta Ingila a shekarar 1954.

A shekarar 1955 ya samu damar karo karatu ta hanyar gidauniyar Ford ya samu tafiya kwas na wata shida kan al’amarin da ya shafi harkar talla da kasuwanci  a makarantar kasuwanci ta jami’ar  Harbad .

Za mu ci gaba makon gobe

 


Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

Kotun Daukaka Kara Za Ta Fara Sauraren Karar Zaben Gwamnan Kano A Ranar Litinin

Next Post

Sirrin Ganyen Gwanda Wajen Gyaran Gashi

Related

Yadda Cinikin Bayi Ya Fara A Nahiyar Afirka (1)
Tarihi

Yadda Cinikin Bayi Ya Fara A Nahiyar Afirka (1)

4 weeks ago
Tarihin Shugaannin Kasar Mali Na Farko A Daular Songhai (8)
Tarihi

Tarihin Shugaannin Kasar Mali Na Farko A Daular Songhai (8)

3 months ago
Tarihin Shugaban Ƙasar Mali Na Farko Sundiata Keita (2)
Tarihi

Tarihin Shugabannin Ƙasar Mali Na Farko A Daular Songhai (7)

3 months ago
A-Ula: Dadadden Birni Mai Cike Da Dinbin Tarihi Da Al’adu
Tarihi

A-Ula: Dadadden Birni Mai Cike Da Dinbin Tarihi Da Al’adu

9 months ago
gusau
Tarihi

Tarihin Gusau Da Sarakunanta (1)

12 months ago
A Tsame Masarautunmu Daga Siyasa
Al'adu

A Tsame Masarautunmu Daga Siyasa

1 year ago
Next Post
Sirrin Ganyen Gwanda Wajen Gyaran Gashi

Sirrin Ganyen Gwanda Wajen Gyaran Gashi

LABARAI MASU NASABA

‘Yansanda Sun Ceto Mutum 21 Da Aka Sace, Sun Kwato N4.8m Kuɗin Fansa

‘Yansanda Sun Damke Mutum Shida Kan Kisan Da Aka Yi A Kasuwar Abuja

July 12, 2025
Sojoji Sun Cafke Wani Soja Kan Mutuwar Mai Gyaran Waya A Adamawa

Sojoji Sun Cafke Wani Soja Kan Mutuwar Mai Gyaran Waya A Adamawa

July 12, 2025
Kotu Ta Umarci Majalisar Dattijan Nijeriya Da Ta Gaggauta Janye Dakatarwar Da Ta Yi Wa Natasha

Lauyoyin Natasha Sun Buƙaci Ta Koma Majalisa Ranar Talata Bayan Miƙa Takardun Hukuncin Kotu

July 12, 2025
Wa’adin Da Tinubu Ya Bai Wa Manoman Da Suka Ci Bashin ‘Anchor Borrowers’ Ya Cika

Dalilin Ware Naira Biliyan 19.5 Da Asusun Bunkasa Aikin Noma Ya Yi

July 12, 2025
Nazari Kan Taraktoci 2,000 Da Tinubu Ya Kaddamar Don Bunkasa Noma

Nazari Kan Taraktoci 2,000 Da Tinubu Ya Kaddamar Don Bunkasa Noma

July 12, 2025
Kashim Shettima Ya Mayar Da Martani Kan Tsadar Rayuwa

Rashin Ganin Shugabannin APC Yayin Ziyarar Shettima A Kano Ya Haifar Da Zazzafar Muhawara

July 12, 2025
Sin Na Goyon Bayan G20 Ta Ci Gaba Da Ba Da Kyakkyawar Gudummawa

Sin Na Goyon Bayan G20 Ta Ci Gaba Da Ba Da Kyakkyawar Gudummawa

July 11, 2025
Hadakar Jam’iyyar ADC Ta Fara Dusashe Karfin PDP A Wasu Jihohin Nijeriya

Hadakar Jam’iyyar ADC Ta Fara Dusashe Karfin PDP A Wasu Jihohin Nijeriya

July 11, 2025
Kasar Sin Na Da Muradin Zurfafa Hadin Gwiwar BRI Da Masar 

Kasar Sin Na Da Muradin Zurfafa Hadin Gwiwar BRI Da Masar 

July 11, 2025
Nijeriya Na Fuskantar Siyasa Mara Tabbas —  Peter Obi

2027: Takarar Shugaban Kasa Zan Yi Ba Mataimaki Ba – Peter Obi

July 11, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.