Sarkin Katsina Muhammadu Dikko ya gina Asibiti da makarantar Boko wadda ita ce ta farko a tarihin ilimi a Arewacin Nijeriya a shekarar 1922 da ake kira da suna Katsina College(Kwalej).Har ila yau Sarkin Katsina Muhammadu Dikko ya daukaka ilimin Boko saboda ai ya tura ‘ya’yansa da sauran wasu su yi karatun Boko,wanda a lokacin ake matukar kyama,a karkashin Turawan mulkin mallaka na kasar Ingila.
A shekarar 1935, Sarkin Katsina Muhammadu Dikko ya rushe Masallacin da Usman Dallaje ya gina lokacin mulkin Dallazawa wanda Umarun Dallaje ya gina, ana kiran Masallacin da sunan Masallacin Dutsi.Shi ne kuma Sarkin Katsina na farko ya tafi aikin Hajji cikin mota a shekarar 1921,daga can kuma shi ne Sarki na farko wanda ya fara tafiya zuwa Ingila,inda shi da ‘yan tawagarsa suka gana da King George V, ya kuma kai ziyara zuwa shahararren gidan namun dajin nan da ake kira da suna London Zoo ko gidan namun daji,ya sake komawa Ingila a shekarun 1924 da kuma 1937.
- ‘Yansanda Sun Daƙile Yunƙurin Yin Garkuwa Da Mutane A Katsina
- Radda Ya Raba Wa Manoma Taki A Jihar Katsin
Bayan da kasar Birtaniya ta mamaye Katsina,Katsina ba tada wata matsalar yaki da kowa.Muhammadu Dikko wanda shi ya iya hawan Doki sai ya bada karfi a rika amfani da Dawakin da ake amfani da su wajen yaki,a rika yin wasa da su kamar Polo .Dikko ya gina babban filin wasa na Polo wanda har yanzu ana amfani da shi a Katsina.Sarkin Katsina Muhammadu Dikko ya ba, ‘ya’yansa da sauran wasu mutane kwarin gwiwa na su yi wasan na Polo .Wanda ya gaji Sarkin Katsina Muhammadu Dikko mai suna Usman Nagogo,ya kai ga nasarar samun kwarewa a wasan na Polo wanda wani dan wasan Polo daga Afirka ya taba samu/kaiwa.Marigayi Sarkin Katsina Usman Nagogo shi ne Shugaban kungiyar masu wasan kwallon Polo na Nijeriya.
Rasuwa da wanda ya gaje shi
Sarkin Katsina Muhammadu Dikko Allah ya yi ma shi rasuwa,a shekarar 1944 da ba’a dade da shigarta ba,bayan ya sanu damuwa daga rashin lafiya, wannan shi yasa aka fara fafutukar neman wanda zai gaje shi.Ta bnagare daya akwai gidan Sarautar Dallazawa a karkashin jagorancin Yarima, wanda shi dan Sarkin Katsina Abubakar ne wanda yake ganin Sarautar Katsina wata dama ce ta shi,sai ta daya bangaren kuma akwai ‘ya’yan marigayi Sarkin Katsina Muhammadu Dikko,wadanda su ma suna da matukar karfi,wadanda daga cikinsu ma da akwai wata ‘yar jayayya kan wanda zai gaji mahaifin nasu. Watan Maris 1944,sai masu zaben Sarki suka zabi karami daga cikin ‘ya’yan Dikko da ake kira da suna Usman Nagogo,wanda shi ne Turawan mulkin mallaka na Ingila suke so saboda yana da ilimin Boko,da kuma yadda ya kasance kusa da mahaifinsa.An nadawa Usman Nagogo rawanin Sarautar ranar 19 Mayu 1944 Yayin da shi kuma marigayi Sarkin Katsina Muhammadu Dikko aka rufe shi,a Lambun da ke fadar Sarkin Katsina Dikko
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp