Taron hadin gwiwa tsakanin kasashen Larabawa da Musulunci ya nanata kiransa ga shugabannin kasashen duniya wajen neman kawo karshen yakin da ake yi a Gaza da Lebanon.
Wannan kiran na daga cikin kudurin da aka fitar bayan wani babban taron hadin gwiwa tsakanin kasashen Larabawa da Musulunci, wanda ya gudana a birnin Riyadh na kasar Saudiyya a ranar 11 ga watan Nuwamba, 2024.
- Gwamnatin Kano Ta Ƙaryata Ciwo Bashin Naira Biliyan 177 Daga Faransa
- Mutane 6 Sun Rasu Sakamakon Ruftawar Ramin Haƙar Ma’adinai A Filato
Hakan na kunshe ne acikin wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga ya fitar, inda shugaba Bola Tinubu da sauran shugabannin kungiyar hadin kan kasashen musulmi (OIC) da kungiyar kasashen Larabawa suka halarci taron.
In ba a manta ba, an kafa kwamitin hadin gwiwa na ministocin kasashen Larabawa da Musulunci, karkashin jagorancin Masarautar Saudiyya, ta hanyar wani kuduri a taron hadin gwiwar Larabawa da Musulunci na farko da aka yi a birnin Riyadh a ranar 11 ga watan Nuwamba, 2023.
Kwamitin ya hada da ministocin harkokin wajen Nijeriya, Masar, Qatar, Turkiyya, Indonesia, Falasdinu, da kuma Jordan.
A cikin kudurinsa na karshe, taron ya bukaci kwamitin ministocin da ya “kara kaimi da fadada mambobinsa da zimmar kawo karshen Ta’addancin Isra’ila a Lebanon da Gaza.”