Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa ba yawon sharholiya ce ta kai Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ‘yan tawagarsa a taron Majalisar Ɗinkin Duniya kan sauyin yanayi da ake yi a Dubai ba, kowa da aikin da zai yi a yayin taron.
Ministan Yaɗa Labarai Da Wayar Da Kai, Alhaji Mohammed Idris ne ya bayyana hakan acikin wata sanarwa da ya rabawa manema labarai inda ya yi raddi kan masu zargin gwamnatin tarayya da fita da mutane fiye da kima zuwa taron na COP28 da ya gudana a kasar Dubai.
- Sin Ta Sake Zama Memba A Rukunin A A Kungiyar IMO
- Kasar Sin: Yawan Kunshin Kayayyaki Da Aka Isar A Kasar Ya Kafa Wani Sabon Tarihi
Idris ya ce gwamnati ta lura da maganganun da ake yi kan adadin ‘yan tawagar da su ka je Dubai domin halartar taron, kuma ta ga “akwai buƙatar ta samar da ƙarin haske kamar yadda ta yi alƙawarin za ta riƙa gudanar da al’amuran ta a bayyane tare da kasancewa mai fayyace komai ga jama’a dangane da abin da ya ke bukatar karin haske”
A cewarsa, “Taron Masu Ruwa da Tsaki (Convention of Parties, COP) na Tsarin Shirye-shiryen Majalisar Ɗinkin Duniya kan Sauyin Yanayi, ‘UNFCCC’ shi ne mashahurin Taron Duniya kan Sauyin Yanayi wanda a bana ya samu halartar fiye da mutane 70,000 daga kasashe fiye da 100. Wakilcin da Nijeriya ta samu ya yi daidai da matsayinta na jagora mai faɗa a ji a Nahiyar Afirka kuma babbar mai taka rawa kan al’amarin sauyin yanayi, wato ‘climate action’.”
Ya ce waɗanda su ka halarci taron daga Nijeriya sun haɗa da jami’an gwamnati, wakilan ‘yan kasuwa da na ƙungiyoyi masu zaman kansu, da ‘yan sa kai, gwamnatocin jihohi, ‘yan jarida, hukumomin ƙasa da ƙasa, wakilan al’ummomin da sauransu.
Idris ya bada lissafin ‘yan tawagar da su ka je a aljihun gwamnati su mutum 422, kamar haka:
idris ya bayyana cewa, Mutane 422 ne kacal suka halarci taron acikin aljihun gwamnati. Wadanda suka hada da Hukumar Sauyin Yanayi ta Ƙasa, 32; Ma’aikatar Muhalli ta Tarayya, 34; Dukkan Ma’aikatu, 167; Fadar Shugaban Ƙasa, 67; Ofishin Mataimakin Shugaban Ƙasa, 9; Majalisar Tarayya, 40 sai kuma Hukumomin gwamnati da cibiyoyi, 73.
Ya bada tabbacin cewa a matsayin Nijeriya na wadda ta ke da ƙarfin tattalin arziki fiye da sauran ƙasashen Afrika kuma mafi yawan jama’a a nahiyar, kuma ta na da tattalin arziki da ake samu daga ma’adinai, wadda ke fuskantar barazanar sauyawar yanayi, ta na da muhimmin matsayi a batun sauyin yanayi, “don haka rawar da za mu taka a taron CCOP28 ba kaɗan ba ce.”
Ministan ya ƙara da cewa: “Taron COP28 ya bada damarmaki na zuba jari da ƙulla yarjejeniyoyin haɗin gwiwa a sassa daban-daban da sauyin yanayi ya shafe su, kuma yanzu haka Nijeriya ta fara cin moriyar shiga taron da ta yi, kamar yadda waɗannan al’amurran su ka shaida:
“Nijeriya da Jamus sun rattaba hannu kan gaggauta aiwatar da Shirin Shugaban Ƙasa kan Wutar Lantarki (PPI) domin inganta samar da lantarki a Nijeriya.
“Shugaba Tinubu ya jagoranci wani babban taro wanda masu ruwa da tsaki da masu zuba jari su ka yi kan Kasuwar Man Fetur ta Nijeriya da Shirin Kawo Motocin Sufuri masu aiki da hasken Rana a lokacin da ake taron ƙoli na COP28 kan sauyin yanayi.
“Akwai alamun Nijeriya za ta ci moriyar Asusun Asara Da Ɓarna (Loss and Damage Fund) wanda aka kafa a lokacin taron COP27 da aka yi a Masar kuma aka ƙaddamar da shi a wajen buɗe wannan taron na COP28 a Dubai. Asusun zai samar da kuɗaɗen da ba bashi ba ne waɗanda za a kashe don tallafa wa ƙasashen da tasirin sauyin yanayi ya fi shafarsu.
“Haka kuma, Shugaban Ƙasa ya yi taro da Shugaban Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE) don tabbatar da yarjejeniyoyin da ke akwai a tsakanin ƙasashen biyu. Duk wannan ban da fa tattaunawar diflomasiyya da aka yi da ƙasashe da ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa daban-daban.”
“Ya kamata a sani cewa, a tsawon shekaru, Nijeriya ta tabbatar da matsayin ta kan batun sauyin yanayi ta hanyar zama ƙasar Afrika ta farko da ta ƙaddamar da Tsarin Tafiyar da Makamashi (Energy Transition Plan), kuma ƙasar Afrika ta farko da ta fitar da Dukiyar Ƙasa Kan Daina Amfani da Makamashin Mai (Sovereign Green Bond), sannan ta na cikin ƙasashe na farko da su ka kafa dokar sauyin yanayi ta ƙasa.
“Saboda haka, muka fitar da wannan karin haske game da cece-kucen da ake yi na tafiya da mutane fiye da kima zuwa taron COP28, Shugaba Tinubu da sauran jami’an Gwamnatin Tarayya sun je Dubai ne domin gudanar da aiki tukuru ba sharholiya ba.”