• English
  • Business News
Wednesday, November 5, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Tashar Sararin Samaniyar Sin Za Ta Kasance “Gida Cikin Sararin Samaniya” Ga Dukkanin Bil Adama

by CMG Hausa
3 years ago
Sin

Da misalin karfe 3 da minti 37 na yammacin jiya Litinin 31 ga watan Oktoba, kasar Sin ta yi nasarar harba bangare na uku, na tashar binciken sararin samaniyarta da ake kira Mengtian zuwa sararin samaniya.

Sa’an nan, bayan kimanin minti 8, dakin gwaje-gwaje na Mengtian ya rabu da rokar Long March-5B, ya kuma shiga hanyarsa kamar yadda aka tsara.

  • Ƙungiyar Tsofaffin Ɗaliban Makarantar ‘Family Support Programme’ Ta Shirya Taron Lakcoci Ga Ɗalibai Sama Da 100 A Katsina

Lamarin da ya nuna cewa, yawan dakunan gwaje-gwaje na tashar binciken sararin samaniya ta kasar Sin, sun karu daga guda biyu zuwa guda uku, wadanda za su kasance tamkar “siffar T”, matakin dake kara kusanto ga aikin kammala tashar.

Aikin gina tashar binciken sararin samaniyar ya kasance muhimmin mataki a aikin sararin samaniyar kasar Sin, inda kasar Sin ke tsayawa tsayin daka wajen raya aikin bisa manufofin amfani da albarkatun sararin samaniya ta hanyar zaman lafiya, da nuna adalci don cimma moriyar juna, da kuma bunkasa harkokin dake da nasaba da hakan cikin hadin gwiwa.

Kana, cikin tarihin bil Adama, tashar binciken sararin samaniya ta kasar Sin, ita ce tasha ta farko da aka bude ga dukkanin mambobin MDD.

LABARAI MASU NASABA

CIIE Na Sin Karin Tagomashi Ne Ga Kasashen Afrika

Sin Ta Kaddamar Da Kwas Din Horon Fasahar Gwaje-Gwaje A Cibiyar CDC Ta Afrika

A halin yanzu, kasar Sin ta bayar da izinin yin gwaje-gwaje a tasharta ga shirye-shirye guda 9, da kasashe guda 17, da kamfanoni guda 23. Lamarin da ya nuna aniyar kasar Sin ta inganta dunkulewar dukkanin bil Adama a fannin habaka aikin sararin samaniya.

Albarkatun sararin samaniya sun zama albarkatu ga dukkanin bil Adama, ya kamata a yi amfani da su wajen tallafawa dukkanin bil Adama. Bayan an kammala aikin gina tashar binciken sararin samaniyar kasar Sin, za a shiga matakin amfani, da kuma raya tashar na tsawon shekaru 10.

Kana, kafin karshen shekarar bana, kasar Sin za ta kuma harba kumbo mai dauke da kayayyaki na Tianzhou mai lamba 5, da kumbo mai dauke da mutane na Shenzhou mai lamba 15, ta yadda ’yan sama jannati guda 6 za su yi aiki tare cikin tashar.

Ana da imanin cewa, a nan gaba, tashar binciken sararin samaniyar kasar Sin za ta kasance “sabon gida cikin sararin samaniya” ga dukkanin bil Adama, inda za su gudanar da aikin binciken sararin samaniya cikin hadin gwiwa.

Cikin tashar, ’yan sama jannati na kasar Sin da na kasashen waje, za su ba da gudummawar binciken sararin samaniya cikin hadin gwiwa, yayin da ake karfafa aikin yin amfani da albarkatun sararin samaniya cikin lumana. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

CIIE Na Sin Karin Tagomashi Ne Ga Kasashen Afrika
Daga Birnin Sin

CIIE Na Sin Karin Tagomashi Ne Ga Kasashen Afrika

November 5, 2025
Sin Ta Kaddamar Da Kwas Din Horon Fasahar Gwaje-Gwaje A Cibiyar CDC Ta Afrika
Daga Birnin Sin

Sin Ta Kaddamar Da Kwas Din Horon Fasahar Gwaje-Gwaje A Cibiyar CDC Ta Afrika

November 4, 2025
‘Yan Sama Jannatin Kumbon Shenzhou-20 Za Su Dawo Doron Kasa A Gobe Laraba
Daga Birnin Sin

‘Yan Sama Jannatin Kumbon Shenzhou-20 Za Su Dawo Doron Kasa A Gobe Laraba

November 4, 2025
Next Post
EFCC Ta Cafke Wani Dan Siyasa Da Wasu Kan Satar Kudin Banki N1.4bn A Jihar Kogi

EFCC Ta Cafke Wani Dan Siyasa Da Wasu Kan Satar Kudin Banki N1.4bn A Jihar Kogi

LABARAI MASU NASABA

Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya Bai Yadda Da Tauye Haƙƙin Addini Ba – Minista

Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya Bai Yadda Da Tauye Haƙƙin Addini Ba – Minista

November 5, 2025
…ACF Ta Nesanta Kanta Da Goyon Bayan Akpabio

Majalisar Dattawa Ta Amince da Naira Tiriliyan 1.1 Don Biyan Bashin ‘Yan Kwangila – Akpabio

November 5, 2025
An Nemi Kasashen ECOWAS Su Samar Da Kariya Ga Yankunan Hakar Ma’adanai

ECOWAS Ta Ƙaryata Iƙirarin Trump Kan Kisan Kiristoci A Nijeriya

November 5, 2025
Tsohon Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Ya Rasu Yana Da Shekaru 86

Tsohon Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Ya Rasu Yana Da Shekaru 86

November 5, 2025
Ɗan Majalisar Amurka Ya Zargi Kwankwaso Da Hannu A Kisan Kiristoci A Nijeriya

Ɗan Majalisar Amurka Ya Zargi Kwankwaso Da Hannu A Kisan Kiristoci A Nijeriya

November 5, 2025
Sanata Barau Ya Tsaya Takarar Shugaban Majalisar Dattawa

Ba Na Jin Tsoron Trump – Martanin Sanata Barau Ga Akpabio

November 5, 2025
CIIE Na Sin Karin Tagomashi Ne Ga Kasashen Afrika

CIIE Na Sin Karin Tagomashi Ne Ga Kasashen Afrika

November 5, 2025
Ma’aikatar Yaɗa Labarai Da BoS Ta Kaduna Sun Ƙulla Yarjejeniyar Samar Da Sahihan Bayanai Ga Al’umma

Ma’aikatar Yaɗa Labarai Da BoS Ta Kaduna Sun Ƙulla Yarjejeniyar Samar Da Sahihan Bayanai Ga Al’umma

November 4, 2025
Sin Ta Kaddamar Da Kwas Din Horon Fasahar Gwaje-Gwaje A Cibiyar CDC Ta Afrika

Sin Ta Kaddamar Da Kwas Din Horon Fasahar Gwaje-Gwaje A Cibiyar CDC Ta Afrika

November 4, 2025
‘Yansanda Sun Kashe Masu Garkuwa Da Mutane 8, Sun Kubutar Da Mutane 3 A Jihar Bauchi

‘Yansanda Sun Ceto Mutane 3 Da Aka Sace A Kwara

November 4, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.