Wani shirin fim mai suna, “Essential Muhammadu Buhari,” shirin Talabijin ne na tsawon sa’a daya game da Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari, tunaninsa, rayuwarsa da falsafarsa, za a fara haska shi a tashoshin talabijin da YouTube daga ranar Lahadin nan 1 ga Janairu, 2023.
A cewar wata sanarwa dauke da sa hannun babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan kafafen yada labarai, Garba Shehu, a ranar Asabar, ya ce shirin fim din shiri ne da shugaban ya bayyana wa wasu ‘yan uwa da abokan arziki da yayin wani taro.
- Shugaba Buhari Ya Amince Da Siyo Motocin Sulke Don Yaki Da ‘Yan Ta’adda
- Zan Yi Nesa Da Abuja Da Zarar Na Bar Mulki —Buhari
Sanarwar ta kara da cewa za a rika nuna shirin na tsawon kwanaki biyu a gidajen Talabijin na cikin gida guda shida.
“Za a nuna a hanyoyin sadarwar TV na kasa a waɗannan lokutan:
“Channel TV 6-7:00na dare, Lahadi 1, ga Janairun, 2023; Nigerian Television Authority, NTA 8-9:00 na dare, Lahadi 1, ga Janairun, 2023; TVC 4:30-5:30 na dare, Lahadi 1, ga Janairun, 2023; Tashi TV 5- 6 na yamma, Litinin 2 ga Janairu; Trust TV 6-7 na yamma, 2 ga Janairu, da African International Television, AIT 8-9:00 na yamma, Lahadi 1 ga Janairu da 8-9:00 na yamma 2 ga Janairu.
Shehu ya kara da cewa “Ku ci gaba da kasancewa tare da mu.” Cewarsa.