Ƙungiyar Ahlul-Baiti da ke Kaduna ta bayyana godiya ga Allah Maɗaukakin Sarki bisa yadda aka gudanar da tattakin Arba’in na shekarar 2025 cikin lumana da nasara, wanda Harkar Musulunci ƙarƙashin jagorancin Sheikh Ibrahim Zakzaky ta saba gudanarwa duk shekara a dukkan sassan ƙasar nan da ma ƙasashen ƙetare.
Duk da irin ƙalubalen da tattakin ya fuskanta a shekarun baya, na bana ya samu halartar ’yan uwa musulmi masu yawa da suka gudanar da tattakin cikin natsuwa, lumana da nuna alhini da sadaukarwa.
- Waye Zai Lashe Kyautar Ballon d’Or?
- Zaɓen Cike Gurbi: Jauro APC Ne Ya Lashe Kujerar Ganye Ta Adamawa – INEC
A cikin wata sanarwa da ƙungiyar ta Ahlul-baiti ta Nijeriya reshen jihar Kaduna ta fitar, ta yi kira ga Gwamnatin Nijeriya da ta amince da kuma mutunta ‘yancin da tsarin mulki ya tanada na ’yancin addini. Ta buƙaci gwamnati da ta ƙara fahimtar harkokin Harkar Musulunci.
Sanarwar ta ƙara da cewa, “Tattakin na wannan shekara shaida ce ta jajircewa, dogewa, son zaman lafiya da balagar da yawa daga cikin ’yan uwa na ita Harkar Musulinci a Nijeriya, wajen kiyaye tsari da martabar addini.”
“Muna amfani da wannan dama domin kira ga gwamnatin Nijeriya da ta ci gaba da kiyaye haƙƙin ’yan ƙasa na ‘yancin addini tare da nuna fiye da haka wajen fahimta, haƙuri, da shiga tattaunawa da Harkar Musulinci. Mutuntawa da buɗe hanyoyin tattaunawa, suna da matuƙar muhimmanci wajen ɗorewar zaman lafiya, haɗin kan ’yan ƙasa, da ci gaba”, inji sanarwar.
Ƙungiyar Ahlul-Baiti ta yi addu’ar ruhin Insaniyya da sadaukarwa da ke tattare da ranar Arba’in ta Imam Hussain (AS) ta zama sila na samar da adalci, da gaskiya a zukatanmu da kuma ƙasarmu baki ɗaya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp