Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Olayemi Cardoso, ya ce tattalin arziƙin Nijeriya yana farfaɗowa tare da ƙara ƙarfi.
Ya bayyana haka ne yayin wani taron manema labarai bayan kammala taron kwamitin kula da manufofin kuɗi karo na 300 a birnin Abuja.
- Gwamnatin Kano Ta Hana Tallace-tallacen Magungunan Gargajiya A Fina-finai Da Kan Tituna
- Xi Ya Aike Da Wasikar Taya Murna Ga Dandalin SCO Na 2025
Cardoso ya ce ƙwarin gwiwar masu zuba jari a Naieriya ya ƙaru cikin watanni 18 da suka gabata, domin masu zuba jari ba sa son ƙasashen da tattalin arziƙinsu ke cikin ruɗani.
Ya ƙara da cewa kwanciyar hankali na tattalin arziƙi yana janyo saka jari da bunƙasar ƙasa.
Sai dai ya ce hauhawar farashi har yanzu na daga cikin ƙalubalen da ake fuskanta, amma ana aiki don magance matsalar.
A baya-bayan nan, Bankin Duniya ya ce tattalin arziƙin Nijeriya ya ƙaru da kashi 3.4 cikin 100 a shekarar 2024, alamar cewa tattalin arziƙin na farfaɗowa.