Bankin Duniya ya bayyana cewa tattalin arziƙin Nijeriya ya ƙaru da kashi 3.9 a rabin farko na shekarar 2025, sakamakon sauye-sauyen da gwamnatin ƙasar ta aiwatar, kamar cire tallafin man fetur da daidaita farashin musayar kuɗaɗen waje.
Bankin ya ce waɗannan matakai sun taimaka wajen daidaita tattalin arziƙin ƙasar tare da ƙara wa Nijeriya ƙarfin jawo hankalin masu zuba jari.
- Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko
- Kwastam Ta Kama Lita 35,000 Na Man Fetur, Tabar Wiwi Da Sauran Kayayyaki A Kebbi
Sai dai Bankin ya nuna cewa wannan ci gaban bai kai ga inganta rayuwar ‘yan Nijeriya ba, musamman masu fama da talauci, hauhawar farashin kayan abinci da tsadar rayuwa.
Ya ce fa’idar waɗannan sauye-sauye dole ta isa ga talakawa kai-tsaye.
Bankin Duniya ya shawarci gwamnati da ta fi mayar da hankali wajen rage hauhawar farashin abinci, yin gaskiya da kuma faɗaɗa shirye-shiryen tallafi da zai kai ga talakawa.
Haka kuma, ya jaddada buƙatar ƙara zuba jari a fannin ilimi, lafiya, da gine-gine don samar da ci gaba mai ɗorewa.
Bankin ya ƙara da cewa, idan gwamnati ta ci gaba da aiwatar da waɗannan sauye-sauyen cikin tsari, tattalin arziƙin Nkjeriya zai iya ƙaruwa zuwa kashi 4.4 nan da shekarar 2027.