Bankin Duniya ya bayyana cewa tattalin arziƙin Nijeriya ya samu gagarumin ci gaba fiye da yadda ake tsammani cikin shekarar 2024, wanda hakan ya sa ci gaban ya fi kowace shekara cikin shekaru 10 da suka gabata.
A wata sanarwa da ya fitar ranar 13 ga watan Mayu 2025, bankin ya ce tattalin arziƙin cikin gida ya tashi da kashi 4.6 cikin 100 a zangon ƙarshe na shekarar 2024, wanda ya haifar da jimillar ci gaban shekara zuwa kashi 3.4 cikin 100 — mafi girma tun shekarar 2014.
- Binciken Jin Ra’ayoyi Na CGTN: Ma’aikatar Harkokin Wajen Sin Ta Ce Harajin Fentanyl Ya Gurgunta Hadin Gwiwar Amurka Da Sin Kuma Fiye Da Kashi 90% Na Jama’a Sun Koka Da “Jarabar” Amurka Ta Cin Zarafi
- Masarautar Saudiyya Ta Raba Magunguna Kyauta Ga Masu Matsalar Ido A Jihar Yobe
Wannan ci gaban, a cewar bankin, ya samo asali ne daga ci gaban da aka samu a ɓangaren mai da iskar gas, ƙarin zuba jari daga masu hannun jari, da ci gaban fasahar zamani da harkokin kuɗi.
Sai dai bankin ya bayyana damuwarsa game da yadda tsadar kayayyaki da matsin rayuwa ke ci gaba da addabar miliyoyin ‘yan Nijeriya.
Ya ce ɓangaren noma ya samu ƙaramin ci gaba ne kawai, da kashi 1.2 cikin 100, saboda rashin tsaro a yankunan da ake noma da tsadar kayayyakin aikin gona kamar taki da fetur.
Wannan matsala, in ji bankin, na shafar samar da abinci da kuma ƙara hauhawar farashin kayan masarufi a kasuwa.
Bankin Duniya ya yaba wa gwamnatin Bola Ahmed Tinubu bisa matakan da ta ɗauka tun bayan da ya hau mulki a watan Mayun 2023, musamman cire tallafin man fetur da yunƙurin ƙarfafa darajar Naira.
Amma bankin ya nuna cewa duk da irin waɗannan gyare-gyare, talakawa na fuskantar matsin rayuwa saboda tashin gwauron zabi da hauhawar farashin kayayyaki.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp