Bisa bayanan da hukumar kididdiga ta kasar Sin ta fitar a yau Litinin, tattalin arzikin kasar ya ci gaba da farfadowa a watan Mayun bana, tare da daidaiton karuwar samar da kayayyaki, da dorewar farfadowar bukatu, da tsayayyen aikin yi da farashi baki daya, da daidaita kudaden kasa da kasa, da ci gaba da sauye-sauye da kara ingantawa, da kuma daidaituwar ayyuka baki daya.
Samar da hajoji daga masana’antu yana bunkasa cikin sauri, kuma masana’antar ba da hidima na ci gaba da farfadowa. A watan Mayu, karin darajar manyan masana’antu a kasar Sin ya karu da kashi 5.6 cikin dari idan aka kwatanta da na makamanci lokacin bara, karuwar 0.3% idan aka kwatanta da na watan da ta gabata. Shigowa da fitar da kayayyaki ya karu cikin sauri, kuma ana ci gaba da inganta tsarin cinikayya. A watan Mayu, jimilar kayayyakin shige da fice ya kai kudin Sin RMB Yuan biliyan 3707.7, wanda ya karu da kashi 8.6 cikin dari idan aka kwatanta da na makamanci lokacin bara. (Yahaya)