Mataimakin babban darektan ofishin kula da harkokin kudi da tattalin arziki na kwamitin tsakiya na Jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin Yin Yanlin, ya bayyana cewa, tattalin arzikin kasar Sin ya tsallake mawuyacin hali, ana kuma saran zai bunkasa a shekarar 2023.
Yin Yanlin wanda ya bayyana haka ne, yayin taron dandalin tattaunawa kan harkokin kudi na kasar Sin wato China Wealth Management 50 Forum jiya Asabar a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin, ya ce akwai abubuwa uku da ba zato ba tsammani da suka yi mummunan tasiri ga tattalin arzikin kasar Sin a shekarar 2022, wato annobar COVID-19, rikici na sassa, da munanan mnufofin kudi na Amurka.
Sai dai kuma, Yin ya lura cewa, kamata ya yi kasar Sin ta nuna tabbaci da samun ci gaba baki daya a shekarar 2023, duk da yanayi na rashin tabbas, saboda za a samu karin abubuwan masu dacewa wajen farfado da tattalin arziki.
Ya ce, baya ga saukaka matakan yaki da annobar COVID-19, ana iya tsammanin murmurewar ayyukan tattalin arziki da zamantakewa cikin sauri.
Inganta manufofin, za su kara karfin farfadowar tattalin arzikin. Gwamnatin kasar Sin ta sha alwashin tabbatar da daidaiton ci gaba a fannin kadarori tare da hana takaita yin sayayya. Kuma za a ci gaba da aiwatar da managartan manufofin kasafin kudi da tsaftataccen tsari a shekara mai zuwa, don tallafawa farfado da tattalin arzikin kasar.
Yin ya kammala da cewa, bisa hasashe na dogon lokaci, koma bayan tattalin arziki da aka fuskanta a ‘yan shekarun nan, wani lamari ne kawai na dan wani lokaci da cutar ta haifar, wanda ba zai canza yanayin ci gaban tattalin arzikin kasar Sin na dogon lokaci ba.
Yana mai cewa, farfadowar tattalin arziki cikin sauri yana nan tafe. (Ibrahim)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp