Tattalin arzikin Nijeriya na fuskantar barazanar sakamakon zanga-zangar matsin rayuwa da ta barke. Yayin da kuma hukumomin tsaro suka zama cikin shiri a wasu jihohi, musamman yankin arewa maso yammacin Nijeriya.Â
‘Yansanda da gwamnatoci sun ba da rahoton cewa an samu barnata kadarori, sa-tar kayan jama’a musamman a shaguna a Kaduna, Kano, Filato, da Bauchi, yayin da ‘yan daba suka kwace ragamar zanga-zangar da aka faro, lamarin da ya janyo tashin hankali.
- Shugaba Tinubu Ya Umurci A Tabbatar Da Daƙile Masu Haƙar Ma’adanai Ba Bisa Ƙa’ida Ba
- Shugaban Timor-Leste Ya Yaba Kayayyaki Kirar Kasar Sin
Kazalika, an cafke masu zanga-zangar a Abuja da wasu sassan jihohin arewa dauke da tutar kasar Rasha. Sai dai hukumomin sun ce sun cafke wasu telolin da ke dinka tutar.
Ofishin jakadancin Rasha da ke Nijeriya ta fito ta ne hannunta daga lamarin, inda ta ce ba ta da masaniya kan masu daga tutar da sunan zanga-zangar matsin rayu-wa a Nijeriya.
Sai dai, shugaban sojojin Nijeriya, Janar Christopher Musa ya ce ba za su lamunci daga tutar wata kasa a cikin Nijeriya ba, ya misalta lamarin da cin amanar kasa.
A tsawon kwanakin da aka yi ana gudanar da zanga-zangar neman kawo karshen gurbataccen shugabanci ya janyo tashin-tashina a Bauchi, Kaduna, da Filato da suka sanya dokar hana fita na awa 24 a baya-bayan nan, yayin da tun a farko ji-hohin Borno, Kano, Katsina, Jigawa, da Zamfara suka ayyana dokar hana zirga-zirga na awa 24 domin dakile tashin hankali da satar dukiyan jama’a.
Sai dai, a Jihar Bauchi a karamar hukumar Katagum ce kawai aka sanya dokar hana zirga-zirgar sabanin sauran jihoji.
Duk da cewa zuwa yanzu wasu jihohin sun sassauta dokar, amma tattalin arziki na samun koma baya a wasu sassan Nijeriya.
Kungiyar kanana da matsakaitan ‘yan kasuwa a Nijeriya (ASBON), ta ce a kalla naira biliyan 600 aka yi asara cikin kwanaki biyar.
Ita ma cibiyar ‘yan kasuwa masu zaman kansu (PPC) ta yi harsashen cewa akwai barazanar rasa naira biliyan 400 kowace rana sakamakon zanga-zangar.
Bayan rasa rayuka da aka samu an kuma samu barnata kadarori da sace kayayya-kin jama’a a shaguna, inda masu zuba jari a kamfanin musaya ta Nijeriya NEL suka rasa biliyan 92 zuwa ranar Litinin.
Rahotonni sun ce shaguna da masana’antu da gidajen mai da dama ne suka kulle sakamakon barazanar zanga-zanga.
Har ila yau, kungiyar masu sayar da man fetur ta IPMAN ta daura alhalin karancin mai da dogon layi da ake samu a ‘yan kwanakin nan kan masu zanga-zangar. Ka-kakin kungiyar IPMAN, Chinedu Ukadike shi ne ya shaida hakan.
Wani kwararren masanin tattalin arziki kuma shugaban SD & D Capital Manage-ment, Gbolade Idakolo, ya shawarci gwamnatin tarayya da ta daura damarar ma-gance bukatun masu zanga-zangar.
Ya ce ta hakan ne kawai za a samu shawo kan matsalolin da zanga-zangar ke ci gaba da haifarwa ga tattalin arziki.
Shi kuma daraktan cibiyar bunkasa harkokin ‘yan kasuwa masu zaman kansu (CPPE), Muda Yusuf, ya roki masu zanga-zangar da su janye domin kauce wa ci gaba da dagula lamarin tattalin arziki.
Ya ce, idan aka yi nazarin halin da tattalin Nijeriya ke ciki, ba bukatar kara dagula lamarin.