A makon da ya gabata ne aka yi hutun bikin “Qingming” na kwanaki uku a kasar Sin, lokacin da Sinawa suka fi zuwa yawon shakatawa a yanayi mai kayatarwa na bazara. Wuraren daban-daban a Sin sun yi kokarin bullo da sabbin matakai na inganta fifikonsu don jawo hankalin masu yawon shakatawa, matakin da kuma ya sa kaimin bunkasuwar tattalin arzikin kasar.
Alkaluman da ma’aikatar al’adu da yawon bude ido ta Sin ta samar a ran 7 ga wata game da yanayin yawon shakatawa a lokacin hutun “Qingming” sun shaida cewa, a tsawon wadannan raneku 3, yawan Sinawa da suka fito don yawon shakatawa a nan cikin gida na kasar Sin ya kai miliyan 126, wanda ya karu da kashi 6.3% bisa na makamancin lokacin bara, sannan yawan kudaden da aka kashe ya haura dala biliyan 7.8, wanda ya karu da kashi 6.7% bisa makamancin lokacin bara.
- Amurka Ta Ƙara Wa Kayayyakin China Haraji Zuwa Kashi 104
- Kasar Sin Na Yaki Da Cin Zalin Da Amurka Ke Yi Ta Hanyar Dora Haraji Ne Bisa Sanin Ya Kamata
Abin lura shi ne, ba da dadewa ba kafin wannan bikin da ya gabata, shugaban kasar Amurka Donald Trump ya sa hannu kan umarnin kakkaba wa sauran kasashen karin harajin kwastam na yi-min-na-rama, inda ya sanar da kakkaba wa dukkanin abokan cinikayyar kasarsa karin harajin kwastam na kashi 10%, tare da kakkaba wa wasu kasashe fiye da hakan. Duk da haka, manufofin da Sin ta dauka a shekarun baya-baya na kyautata tsarin samar da kayayyaki da habaka bukatun cikin gida da tabbatar da tafiyar tattalin arzikin cikin gida yadda ya kamata ba tare da tangarda ba, sun kara samar da kuzarin bunkasar tattalin arzikinta a cikin gida. Bunkasar tattalin arziki mai alaka da harkokin yawon shakatawa a lokacin hutun bikin Qingming ta shaida hakan.
A ran 7 ga watan nan da muke ciki bisa agogon gabashin kasar Amurka, kasar ta Amurka ta kara barazanar kakkaba wa Sin karin haraji na kashi 50%, kasar Sin a nata bangaren ta bayyana aniyarta ta daukar matakan da suka dace don kare muradunta.
Tattalin arzikin Sin na samun bunkasa yadda ya kamata duk da matakin kakkaba mata karin harajin kwastam da Amurka ke dauka, kamar yadda shugaban kasar Mr. Xi Jinping bayyana cewa: “Tattalin arzikin Sin ya yi kama da teku a maimakon karamin tabki.” Teku ba ya tsoron mahaukaciyar guguwa, kuma yana iya tinkarar duk wasu kalubale daga waje. (MINA)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp