A baya-bayan nan, hukumomin hada-hadar kudi na kasa da kasa masu yawa sun daga hasashen bunkasuwar tattalin arzikin Sin na bana. Game da wannan batu, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin ya bayyana a gun taron manema labaru da aka gudanar a yau cewa, a rubu’in farko na shekarar bana, tattalin arzikin Sin ya samu bunkasuwa, inda yawan kudin da ake kashewa da zuba jari da kayayyakin da aka fitar zuwa kasashen waje, ya samu karuwa yadda ya kamata. Haka kuma manyan alamomin ci gaban tattalin arziki, da suka hada da yanayin ayyukan yi da na hauhawar farashin kayayyaki, da kudin dake shiga da fita daga kasa, na bisa madaidaicin matsayi, lamarin dake shaida cewa, tattalin arzikin Sin ya samu karuwa a lokacin bazara.
Wang Wenbin ya yi nuni da cewa, yawan GDP na rubu’in farko na bana na kasar Sin ya karu da kashi 5.3 cikin dari, a cikinsa bukatun cikin gida ya samar da gudummawar kashi 85.5 cikin dari wajen bunkasa tattalin arzikin kasar. Ya kuma yi imanin cewa, bisa samun bunkasuwa mai inganci da bude kofa ga kasashen waje, za a gaggauta kyautata tsarin ci gaban tattalin arzikin Sin yadda ya kamata, wanda zai kara samar da gudummawa ga bunkasuwar tattalin arzikin duniya baki daya. (Zainab Zhang)