Duk da cewa kasar Sin tana fuskantar matsin lamba, sakamakon cutar COVID-19, a hannu guda tattalin arzikin kasar ya kai sabon mataki a shekarar 2022 da ta gabata, kuma an samu daidaito wajen samar da guraben aikin yi, da kuma farashin kayayyaki, kana rayuwar Sinawa ta samu kyautatuwa a kai a kai.
A yau Talata, ofishin watsa labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin ya kira taron manema labarai, inda aka bayyana cewa, sakamakon kididdigar da aka yi ya nuna cewa, jimillar GDPn kasar Sin na shekarar 2022 ya kai kudin Sin yuan biliyan 121020.7, kwatankwacin dalar Amurka triliyan 17.95, adadin da ya karu da kaso 3 bisa dari idan aka kwatanta da na shekarar 2021.
Ban da haka, an samu yabanyar hatsi a shekarar 2022, inda adadin hatsin da kasar ta samu ya kai tan miliyan 686.53, adadin da ya karu da tan miliyan 3.68 bisa na shekarar 2021. Haka zalika, masana’antu, da sana’o’in kere-kire na kasar, sun samu ci gaba cikin sauri, kana ayyukan ba da hidima sun farfado yadda ya kamata. Game da guraben aikin yi kuwa, a shekarar bara adadin guraben ayyukan yi da aka samar ya kai miliyan 12.06. (Mai fassarawa: Jamila daga CMG Hausa)