Bisa alkaluman da aka samu ta hanyar gudanar da kididdiga a matakin farko, jimillar GDP ta kasar Sin a shekarar 2024 ta kusan kai kudin Sin RMB Yuan triliyan 135, wadda ta karu da kaso 5% bisa ta shekarar 2023. Ta wadannan alkaluma za mu iya ganin yadda tattalin arzikin Sin ya kasance cikin wani yanayi mai tagomashi a shekarar 2024, inda kasar ta cika burinta na raya tattalin arziki.
Matakan da kasar Sin ta dauka, wadanda suka taimaka wa raya tattalin arzikinta, sun hada da dogaro kan ingantaccen tsarinta na kera kayayyaki da samar da su ga kasuwa, da manufar bude kofa ga kasashen waje. Kana kasar ta yi hadin kai tare da kasashe daban daban, a kokarin tinkarar barazanar da aka samu sakamakon tasirin wasu kasashe, inda ta raya bangaren cinikin waje, da raba wa sauran kasashe damammaki na samun riba a kasuwannin Sin.
- Babu Dalilin Fargaba Ko Tsoro Don Sanya Wa Mara Lafiya Robar Hanci
- Yadda Kuncin Rayuwa Da Matsalar Tattalin Arziki Ke Kara Haifar Da Rikice-rikice Tsakanin ‘Yan Haya Da Masu Gidaje
Ban da haka, kasar tana kokarin raya sabbin fasahohi masu alaka da masana’antu, don neman samun cikakken karfi a wannan fanni.
Abin lura shi ne, tushen ci gaban tattalin arzikin kasar Sin ya kunshi dimbin bukatun da take samu a cikin gidanta, da wani cikakken tsari na masana’antu, da kuma kwarewar kasar a fannin biyan bukatun kamfanoni. Saboda haka, ko da yake tattalin arzikin Sin na ci gaba da fuskantar kalubale, ganin yadda sauyawar yanayin ketare ke kara yin tasiri, amma matakan da kasar ta dauka na aiwatar da ingantattun tsare-tsaren raya tattalin arziki, da bude kofarta ga karin kasashe, za su taimaki kasar a kokarinta na samun ci gaban tattalin arizki a kai a kai. (Bello Wang)