Ma’aikatar kula da sufuri ta kasar Sin, ta ce tattalin arzikin teku da suka shafi masana’antun yin tafiya ta teku da kamun kifi da kera jiragen ruwa, ya zarce kudin Sin RMB yuan triliyan 9, kwatankwacin dalar Amurka triliyan 1.25, a shekarar 2022.
Ma’aikatar ta fitar da alkaluman ne a yau Talata, yayin wani taro na ranar sufuri ta teku ta kasar Sin karo na 19 da aka yi a birnin Cangzhou dake lardin Hebei na arewacin kasar Sin.
A cewar rahoton ma’aikatar, ana jigilar kimanin kaso 95 na kayayyakin cinikayya tsakanin Sin da kasashen waje ta teku.(Fa’iza)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp