Ministan harkokin wajen kasar Iran, Abbas Araqchi, ya gudanar da ziyarar aiki a kasar Sin daga ranar 27 zuwa 28 ga watan Disambar shekara ta 2024 da ta gabata, inda ya yi shawarwari tare da takwaransa na kasar Sin Wang Yi, da kuma zantawa da wakilin CMG, wato babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin.
A yayin shawarwarin ministocin harkokin wajen na Sin da Iran na wannan karo, sun cimma matsaya daya kan cewa, Gabas ta Tsakiya, yanki ne na al’ummar Gabas ta Tsakiya, a maimakon wani dandali na yin takara tsakanin manyan kasashe. Game da hakan, a tattaunawarsa da wakilin kafar CMG, Araqchi ya ce, al’ummun yankin Gabas ta Tsakiya, ko kuma yammacin Asiya, sun dade suna jin radadi a jikinsu, sakamakon shisshigin da kasashen waje suke yi musu, kana kuma a cewarsa, dukkan matsaloli, da rikice-rikicen dake addabar yankin, sun samo asali ne daga tsoma bakin kasashen waje.
Game da rawar da kasar Sin ke takawa a fannin shimfida zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya, Araqchi ya bayyana cewa, sun ga sahihancin kasar Sin, inda take kiyaye dangantakar tattalin arziki da kasuwanci tare da dukkan kasashen yankin, har ma tana kiyaye kyakkyawar alaka mai ma’ana tare da daukacin kasashe. Ya ce Sin amintacciyar kasa ce da ta cancanci girmamawa, wanda hakan ya sa take iya taka rawa a fannin siyasa a yankin Gabas ta Tsakiya, don lalubo bakin zaren daidaita sabanin kasashen yankin, da taimaka musu wajen samun mafita. (Murtala Zhang)