• English
  • Business News
Saturday, July 5, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Manyan Jigajigan ‘Yan Jam’iyyun Adawa Da Suka Sauya Sheka Zuwa APC A 2024

by Yusuf Shuaibu
6 months ago
in Manyan Labarai
0
Manyan Jigajigan ‘Yan Jam’iyyun Adawa Da Suka Sauya Sheka Zuwa APC A 2024
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Shekarar 2024 ta kasance cike da sauye-sauye daga kowane bangare ciki har da fagen siyasar Nijeriya.

Matsakaici na siyasa ta bude tattaunawar hadewa tsakanin jam’iyyun adawa gabanin zabukan 2027 da kuma ficewar wasu manyan ‘yan siyasa daga jam’iyyunsu zuwa jam’iyyar APC mai mulki a 2024.

Kamar yadda ya zama sananne a siyasar Nijeriya, bayan zabukan 2023, an samu kura-kurai da dama. Masana harkokin siyasa sun suffanta hakan a matsayin karfin daidaituwar kasuwar bukata.

A cikin shekara mai kamawa, akasarin masu sauya shekar sun bayyana jam’iyyar APC a matsayin hanya daya tilo da ta kudiri aniyar magance matsalolin da ke addabar kasar nan.

  • Badakalar Rajistar Olmo: Magoya Bayan Barcelona Sun Fara Yanke Tsammani Da Laporta
  • Kirsimeti: Gwamnatin Kebbi Ta Raba Shinkafa Don Tallafa Wa Kiristoci

Rahotanni da dama sun bayyana cewa ficewar ‘yan siyasa daga wannan jam’iyya zuwa waccan ya zama al’ada a fagen siyasar Nijeriya, wadanda suka yi hakan na da dalilai daban-daban.

Labarai Masu Nasaba

Ku Manta Da 2027, Tinubu Zai Ci Gaba Da Mulki Har 2031 — Fadar Shugaban Ƙasa Ga ADC

Kwankwaso Ba Zai Sake Yi Mana Takarar Shugabancin Ƙasa Ba A Zaɓen 2027 Ba – NNPP

Ga wasu daga cikin fitattun ‘yan siyasar a bangaren jam’iyyun adawa suka sauya sheka zuwa jam’iyya mai mulki a cikin shekarar 2024, sun hada da:

Ramalan Yero

Tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Ramalan Yero ya koma APC, watanni biyar bayan ficewa daga jam’iyyar PDP.

Tsohon gwamnan, wanda ya yi wa al’ummar Kaduna mulki daga shekarar 2012 zuwa 2015 a jam’iyyar PDP, ya koma APC ne a ranar 12 ga Fabrairu, 2024.

Da yake bayar da dalilan ficewarsa, Yero ya ce, “Tun ranar da muka sanar da muka fice daga PDP, jam’iyyun siyasa da dama sun tuntube mu ciki har da APC mai mulki.

“Mun hadu, sannan muka tattauna lamarin. Don haka, daga yau 12 ga Fabrairu, 2024, ni da wakilan sauran ‘yan siyasa mun yanke shawarar komawa APC.”

Anyim Pius Anyim

Tsohon shugaban majalisar dattawan wanda ya ci zabe a jam’iyyar PDP a watan Yulin 2024, Anyim Pius Anyim ya fice daga PDP zuwa jam’iyyar APC mai mulki.

An gabatar da shi ne ga Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a fadar gwamnati da ke Abuja, inda ya shaida wa manema labarai cewa ya kamata a hada kai da juna domin magance matsalolin da suka addabi kasar nan.

Gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodinma ne ya jagorance shi zuwa fadar shugaban kasa tare da wasu jiga-jigan jam’iyyar APC.

 

Emeka Ihedioha

Haka kuma, tsohon gwamnan Jihar Imo, Emeka Ihedioha, wanda ya yi mulki a jihar tsakanin 29 ga Mayu, 2019 zuwa 14 ga Janairu, 2020, daga baya ya fice daga PDP.

Ihedioha, wanda tsohon mataimakin shugaban majalisar wakilai ne ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar PDP a wata wasika da ya aike wa shugaban jam’iyyar a unguwar Mbutu da ke karamar hukumar Aboh Mbaise a Jihar Imo. Wasikar ta kasance mai dauke da kwanan wata 23 ga Afrilu 2024.

Ihedioha ya bayyana cewa ya bayar da gudunmawarsa wajen ci gaban jam’iyyar PDP tun lokacin da aka kafa ta a shekarar 1998.

Daniel Bwala

Shi ma tsohon mai magana da yawun kungiyar yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Daniel Bwala, ya fice daga jam’iyyar zuwa APC a cikin shekarar 2024, yana mai cewa ya jajirce wajen yi wa Shugaba Tinubu aiki kuma ba ya ladama kan hakan.

Bwala ya ce yadda Shugaba Tinubu ya jajirce wajen tunkarar matsaloli da suka addabi kasar nan da suka hada da tsadar gudanar da mulki ya burge shi. Ya yi gaggawar tunatar da jama’a cewa ya kasance a bangaren Tinubu, kuma zai ci gaba da mara masa baya.

A ranar 14 ga Nuwamba, Shugaba Tinubu ya amince da nadin Mista Bwala a matsayin mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai da sadarwa.

An bayyana hakan ne a wata sanarwa da mai bai wa Tinubu shawara na musamman kan yada labarai, Mista Bayo Onanuga ya fitar.

Sylbanus Nguji Ngele

Tsohon mamba a kwamitin ayyuka na jam’iyyar PDP na kasa kuma sanata mai wakiltar Ebonyi ta Arewa a majalisar dokokin kasa a karkashin jam’iyyar PDP, Sylbanus Nguji Ngele ya sauya shaka zuwa APC.

Ya fice daga jam’iyyar ne a watan Mayun 2024, tare da wasu jiga-jigan jam’iyyar a Jihar Ebonyi, wanda ya kasance tsohon dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Abakaliki/Izzi kuma tsohon dan takarar gwamna a zaben 2023, Hon. Sylbester Ogbaga.

An tarbi Ngele da sauran wadanda suka sauya sheka zuwa jam’iyyar APC a wani biki da aka yi a Abakaliki.

Da yake jawabi a wajen taron, Ngele ya bayyana cewa babban dalilinsu na ficewa daga jam’iyyar PDP shi ne rashin iya samar da gwamna daga kabilar Izzi, wanda jam’iyyar APC ta iya cimmawa, daidai da tsarin mulkin Jihar Ebonyi.

Sanata Ezenwo Onyewuchi

Sanata mai wakiltar Imo ta Gabas a karkashin jam’iyyar LP, Ezenwa Francis Onyewuchi, shi ma ya fice daga jam’iyyarsa zuwa jam’iyyar APC mai mulki. Shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio ya karanta wasikar sauya shekar Sanata Onyewuchi a zauren majalisa.

Sanatan na Imo ya dogara ne da sashe na 68 (1g) na kundin tsarin mulki.

‘Yan Majalisa Na LP Da PDP Sun Sauya Sheka Zuwa APC

A ranar 4 ga Disamba, 2024, ‘yan majalisar wakilai hudu daga jam’iyyar LP da daya daga PDP sun sauya sheka zuwa APC.

‘Yan majalisan sun hada da Tochukwu Okere (Jihar Imo), Donatus Mathew (Kaduna), Bassey Akiba (Kuros Ribas), Iyawu Esosa (Edo) da Erthiatake Ibori-Suenu (Delta) da suka fice daga PDP.

A watan Oktoban 2024, APC ta samu karin kujera a majalisar wakilai bayan ficewar Abubakar Gumi daga PDP.

Haka zalika, dan majalisar wakilai, Salman Idris, ya sauya sheka daga jam’iyyar ADC zuwa APC. Yana wakiltar mazabar Kabba Bunu/Ijumu a majalisar tarayya.

Shugaban majalisar wakilai, Tajudeen Abbas ne ya karanta wasikunsu na sauya sheka a zaman majalisar wakilai.

Yana Da Muni Ga Dimokuradiyya – Manazarci

Sai dai wani mai sharhi kan harkokin siyasa, Jackson Lekan Ojo, a wata tattaunawa ta wayar tarho, ya ce batun sauya sheka ya samu karbuwa a kasar nan, amma ya bayyana hakan a matsayin wani mummunan al’amari ga dimokuradiyyar kasar nan.

Ya ce al’amari ne mai matukar damuwa da ya kamata a duba tare da tsauraran matakai na doka don shawo kan lamarin, yana mai jaddada cewa ya kamata shugabannin adawa su ci gaba da kasancewa a cikin jam’iyyunsu don seta jam’iyya mai mulki.

Ojo ya ce kamata a samar da tsarin doka da zai iya hukunta masu aikata lamarin sauya sheka, domin dakile tashe-tashen hankula.

“Hakika mummunan al’amari ne ga dimokuradiyya. Wadannan mutane ne wadanda ke gudanar da gwamnatin lokacin da aka zaba su a karkashin wata jam’iyya, amma sai su sauka sheka domin rashin manufa mai kyau ga kasar nan.

“Suna barin tsohuwar jam’iyyunsu zuwa sababbi saboda son kai. Wannan lamari na sauka sheka daga jam’iyyun adawa zuwa jam’iyya mai mulki abin tsoro ne. Wannan bai dace da dimokuradiyyar kasar nan ba,” in ji shi.

Ojo ya kara da cewa sauye-sauyen da suka biyo bayan makircin siyasa da maslaha ba su da wani tasiri mai kyau ga talakawa da ‘yan siyasa ke neman gudanarwa.


Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: APCPDP
ShareTweetSendShare
Previous Post

Tattaunawar Wakilin CMG Da Ministan Harkokin Wajen Iran

Next Post

Yadda Ittihadil Ummah Ta Gabatar Da Walimar Yaye Dalibai Dattawa Da Suka Sauke Alku’arni A Abuja

Related

Ku Manta Da 2027, Tinubu Zai Ci Gaba Da Mulki Har 2031 — Fadar Shugaban Ƙasa Ga ADC
Manyan Labarai

Ku Manta Da 2027, Tinubu Zai Ci Gaba Da Mulki Har 2031 — Fadar Shugaban Ƙasa Ga ADC

48 minutes ago
Kwankwaso Ba Zai Sake Yi Mana Takarar Shugabancin Ƙasa Ba A Zaɓen 2027 Ba – NNPP
Manyan Labarai

Kwankwaso Ba Zai Sake Yi Mana Takarar Shugabancin Ƙasa Ba A Zaɓen 2027 Ba – NNPP

8 hours ago
Gwamna Ademola Adeleke Ya Ƙaryata Jita-Jitar Sauya Sheƙa Daga PDP Zuwa APC
Manyan Labarai

Gwamna Ademola Adeleke Ya Ƙaryata Jita-Jitar Sauya Sheƙa Daga PDP Zuwa APC

12 hours ago
‘Yansanda Sun Kama Barayi 15, Sun Kwato Motocin Sata 20 A Kano
Manyan Labarai

’Yansanda Sun Kama ’Yan Bindiga 17 Tare Da Kashe 3 A Abuja

1 day ago
Kotu Ta Umarci Majalisar Dattijan Nijeriya Da Ta Gaggauta Janye Dakatarwar Da Ta Yi Wa Natasha
Manyan Labarai

Kotu Ta Umarci Majalisar Dattijan Nijeriya Da Ta Gaggauta Janye Dakatarwar Da Ta Yi Wa Natasha

1 day ago
Zanga-zangar ‘Yan Gudun Hijira Na Yelewata ‘Yar Manuniya Ce Ga Daukar Matakan Da Suka Dace
Manyan Labarai

Zanga-zangar ‘Yan Gudun Hijira Na Yelewata ‘Yar Manuniya Ce Ga Daukar Matakan Da Suka Dace

2 days ago
Next Post
Yadda Ittihadil Ummah Ta Gabatar Da Walimar Yaye Dalibai Dattawa Da Suka Sauke Alku’arni A Abuja

Yadda Ittihadil Ummah Ta Gabatar Da Walimar Yaye Dalibai Dattawa Da Suka Sauke Alku’arni A Abuja

LABARAI MASU NASABA

‘Yan Adawa Sun Dunkule A ADC Don Tunkarar Tinubu A 2027

‘Yan Adawa Sun Dunkule A ADC Don Tunkarar Tinubu A 2027

July 5, 2025
Wakilin Sin Ya Yi Jawabi Game Da Raya Hidimomi Ga Nakasassu Ta Hanyar Fasahar AI A Madadin Wakilan Kasashe Fiye Da 70

Wakilin Sin Ya Yi Jawabi Game Da Raya Hidimomi Ga Nakasassu Ta Hanyar Fasahar AI A Madadin Wakilan Kasashe Fiye Da 70

July 5, 2025
Ku Manta Da 2027, Tinubu Zai Ci Gaba Da Mulki Har 2031 — Fadar Shugaban Ƙasa Ga ADC

Ku Manta Da 2027, Tinubu Zai Ci Gaba Da Mulki Har 2031 — Fadar Shugaban Ƙasa Ga ADC

July 5, 2025
Zan Dade Ban Manta Da Mahaifinmu Ba -Abba Sadau

Zan Dade Ban Manta Da Mahaifinmu Ba -Abba Sadau

July 5, 2025
Kuri’ar Jin Ra’ayin Jama’a Ta CGTN Ta Nuna Goyon Baya Ga Fadadar Kungiyar BRICS A Matsayin Hanyar Bunkasa Hadin Gwiwa

Kuri’ar Jin Ra’ayin Jama’a Ta CGTN Ta Nuna Goyon Baya Ga Fadadar Kungiyar BRICS A Matsayin Hanyar Bunkasa Hadin Gwiwa

July 5, 2025
Gidajen Gala Ne Kadai Mafita Ga Masana’antar Kannywood – Falalu Dorayi

Gidajen Gala Ne Kadai Mafita Ga Masana’antar Kannywood – Falalu Dorayi

July 5, 2025
Wang Yi Da Takwaransa Na Ghana Sun Aikewa Juna Sakon Murnar Cika Shekaru 65 Da Kulla Dangantakar Diplomasiyya A Tsakanin Kasashensu

Wang Yi Da Takwaransa Na Ghana Sun Aikewa Juna Sakon Murnar Cika Shekaru 65 Da Kulla Dangantakar Diplomasiyya A Tsakanin Kasashensu

July 5, 2025
Sin Da Faransa Sun Amince Da Ingiza Cudanyar Mabanbantan Sassa Tare Da Samar Da Karin Tabbaci Ga Duniya

Sin Da Faransa Sun Amince Da Ingiza Cudanyar Mabanbantan Sassa Tare Da Samar Da Karin Tabbaci Ga Duniya

July 5, 2025
Bukatar Ma’aurata Su Rika Bayyana Wa Junansu Gaskiyar Yanayin Samunsu

Bukatar Ma’aurata Su Rika Bayyana Wa Junansu Gaskiyar Yanayin Samunsu

July 5, 2025
Yadda Ake Gasasshen Biredi (Sandwich)

Yadda Ake Gasasshen Biredi (Sandwich)

July 5, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.