Jimilar mambobi 118 na tawagar jami’an bincike da ceto ta kasa da kasa ta kasar Sin (CISAR), ta isa birnin Nay Pyi Taw na Myanmar, jiya Lahadi da dare.
Tawagar ta hada da masana girgizar kasa, da injiniyoyin gine-gine, da ma’aikatan bincike da ceto, da jami’an lafiya, da jami’ai masu aiki da karnuka domin gano mutane. Kuma sun tafi da kayayyakin aiki kamar naurorin gano mai rai, da na rusa gini, da kayayyakin lafiya.
- Ofishin Siyasa Na Kwamitin Tsakiyar Jks Ya Kira Taron Nazarin Ayyukan Kiyaye Muhallin Halittu Da Sauransu
- Sin Ta Gano Babban Yankin Hakar Danyen Mai A Tekun Kudancin Kasar
CISAR wadda aka kafa a 2001, tawaga ce mai shaidar kwarewa ta MDD, kuma ta riga ta gudanar da ayyuka sama da 20 a kasashen duniya.
Ban da haka, da safiyar yau Litinin, kashin farko na kayayyakin jin kai da Sin ta bai wa Myanmar domin rage radadin girgizar kasar da ta auku, ya tashi daga babban filin jirgin saman birnin Beijing.
A martaninta game da bukatar Myanmar, Sin ta yanke shawarar samar wa kasar agajin jin kai na Yuan miliyan 100, kwatankwacin Dala miliyan 13.9, domin rage radadin ibtila’in.
A cewar hukumar raya kasashe ta kasar Sin, kashin farko na kayayyakin ya hada da tantuna da barguna da kayayyakin lafiya. (Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp