Ministan tsaro, Mohammed Badaru da takwaransa na ma’aikatar jin kai da rage radadin talauci, Farfesa Nentawe Yilwatda, a ranar Asabar sun ziyarci al’ummomin da aka kai wa harin ta’addanci a karamar hukumar Bassa ta jihar Filato.
A makon jiya ne wasu da ake kyautata zaton ‘yan bindiga ne suka kai hari a kauyen Zike da ke gundumar Kwall a masarautar Irigwe a garin Bassa inda suka kashe mutane sama da 50.
- Baje Kolin Kayayyakin Masarufi Na Duniya Ya Kara Fito Da Kyawun Kasuwar Sin
- Tawagar CPPCC Ta Ziyarci Nijeriya Da Cote d’Ivoire Da Senegal
Badaru ya jajanta wa iyalan wadanda suka rasa ‘yan uwansu tare da bayyana kudirin gwamnatin tarayya na tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi.
“Mun zo nan ne a madadin gwamnatin tarayya domin ganowa da kuma jajanta muku rashin da aka yi, muna so mu tabbatar muku da cewa jami’an tsaro za su kawo karshen wannan kashe-kashen na rashin hankali.
“An yi mini cikakken bayani, kuma ina so in tabbatar muku cewa mun fahimci tushen wannan batu. Zamu kama wadanda suka aikata wannan aika-aika.
“Shugaban kasa ya damu matuka, kuma ya umarce mu da mu nemo wadanda suka aikata wannan aika-aika domin su fuskanci shari’a, muna aiki tare da gwamnatin jihar domin daukar tsarin da zai hana faruwar wannan mummunan lamari, lokaci ya yi da za a kawo karshen wannan hauka,” inji shi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp