Wata tawaga daga Gwamnatin Tarayya ta halarci jana’izar fitaccen ɗan kasuwa kuma dattijon Arewa, Alhaji Aminu Ɗantata, wadda aka yi a birnin Madina na ƙasar Saudiyya a ranar Talata.
Alhaji Ɗantata ya rasu ne a ranar Asabar a birnin Abu Dhabi, a kasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE), yana da shekara 94 a duniya. Bisa ga wasiyyar sa ne aka binne shi a Madina.
- Ɗantata: Majalisar Dattawa Ta Ɗage Taron Jin Ra’ayin Jama’a A Arewa maso Yamma
- An Gudanar Da Bikin Daga Tuta Da Bikin Murnar Cika Shekaru 28 Da Dawowar Yankin HK Karkashin Kasar Sin
Ɗan sa, Alhaji Tajudeen Ɗantata, da Alhaji Aliko Ɗangote, sun isa Madina a safiyar Talata tare da gawar marigayin, suna tare da wasu ‘yan’uwa na kusa.
Tawagar ta Gwamnatin Tarayya ta bar Nijeriya ne a daren Lahadi, inda suka isa Madina da sanyin safiyar Litinin.
Ministan Tsaro kuma tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Muhammad Badaru Abubakar, shi ne ya jagoranci tawagar.
Cikin tawagar akwai Ministan Shari’a kuma Antoni Janar na Ƙasa, Yarima Lateef Fagbemi, SAN; a Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris; da Ƙaramin Ministan Harkokin Gidaje da Cigaban Birane, Hon. Yusuf Abdullahi Ata; da kuma Hassan Abdullahi, Daraktan Tsaro na Cikin Gida a ofishin Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Tsaro (NSA), wanda ya wakilci NSA.
Wasu fitattun malamai na addinin Musulunci da suka kasance cikin tawagar sun haɗa da Dakta Bashir Aliyu Umar, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, da Limamin Masallacin Ɗantata da ke Abuja, Khalifa Abdullahi Muhammad.
Jami’an Ofishin Jakadancin Nijeriya da ke Jiddah sun haɗu da tawagar, ƙarƙashin jagorancin Ambasada Ibrahim Modibbo, tare da Ambasada Mu’azzam Ibrahim Nayaya, da Manjo Janar Adamu Hassan, waɗanda suka jagoranci shirye-shiryen jana’izar.
Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin, da tsohon Shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Dakta Abdullahi Ganduje, su ma sun halarci jana’izar tare da Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, da na Jigawa, Alhaji Umar Namadi.
Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II da Sarki Aminu Ado Bayero su ma sun halarci jana’izar.
An binne Alhaji Aminu Ɗantata a maƙabartar Baƙiyya da ke Madina bayan an gudanar da sallar jana’iza da yammaci a Masallacin Manzon Allah (SAW).
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp