Tawagar Gwamnatin Tarayya ta isa gidan marigayi Alhaji Aminu Ɗantata a Madina domin isar da saƙon ta’aziyyar Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ga iyalan mamacin.
Ɗantata dai ya rasu ne a birnin Abu Dhabi shekaranjiya Asabar yana da shekaru 94. A gobe Talata za a rufe shi a maƙabartar Baƙiyya ta Madina.
- CAF Za Ta Ƙaddamar Da Sabon Kofin Gasar Ƙasashen Afrika Na Mata
- Cikar MDD Shekara 80: Nasarorinmu Sun Kara Mana Kaimi Da Kyakkyawar Makoma A Nan Gaba
Tawagar gwamnatin Nijeriya ta isa Madina ne yau da safe a ƙarƙashin jagorancin Ministan Tsaro kuma tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Muhammad Badaru Abubakar.
A tawagar akwai Ministan Shari’a, Yarima Lateef Fagbemi, SAN; Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris; da Ƙaramin Ministan Muhalli da Haɓaka Birane, Honorabul Yusuf Abdullahi Ata.
Har ila yau, akwai malamai da suka haɗa da Dakta Bashir Aliyu Umar, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, da Limamin Masallacin Ɗantata da ke Abuja.
A bisa jagorancin Alhaji Mustapha Junaid, iyalan mamacin, da suka haɗa da matan sa da ‘ya’ya da jikokin sa, sun tarbi tawagar, kuma sun yi masu godiya.
Minista Badaru ya miƙa saƙon ta’aziyya daga Shugaba Bola Ahmed Tinubu, yana cewa, “Rasuwar Baba Aminu ta taɓa Shugaba Tinubu matuƙa. Yana addu’ar Allah ya yi masa sakayya da gidan Aljannar Firdausi, kuma yana ba dukkan iyalan sa haƙurin su yi jimirin jure wannan babban rashi.”
Jakaden Nijeriya a Saudi Arebiya, Ambasada Ibrahim Modibbo, da Babban Jagoran Aikin Jakadanci, Ambasada Mu’azam Ibrahim Nayaya, da Jami’in Kula da Tsaro a Ofishin Jakadanci, Manjo Janar Adamu Hassan, duk suna cikin tawagar.
Malaman da aka je da su kuma duk sun yi addu’o’i ga marigayi Alhaji Aminu Ɗantata.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp