Tawaga ta 12 ta jami’an lafiya na kasar Sin, ta kai ziyara kauyen Juba Nabari dake arewacin Juba, babban birnin Sudan ta kudu, domin bayar da kulawar lafiya kyauta ga daruruwan marasa lafiya.
Shugaban tawagar ta 12, Du Changyong, ya ce ziyartar Juba Nabari na da nufin aiwatar da sakamakon dandalin taron tattauna hadin gwiwar Sin da Afrika na 2024 da kuma shirin “Tawagogi 100 na jami’an lafiya a kauyuka 1,000” domin bayar da hidimomin lafiya ga mutanen yankunan karkara.
A cewar Du Changyong, tawagar ta 12 ta isa Sudan ta Kudu ne a watan Satumban 2024, kuma zuwa yanzu, sun kula da marasa lafiya 6,300 da gudanar da tiyata 64 da kula da marasa lafiya 441 dake cikin mawuyacin hali. (Mai fassara: Fa’iza Mustapha)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp