Tawagar manyan malaman addinin musulunci da kwararru mai kunshe da malamai sama da 30, daga kasashe 14, sun fara ziyarar gani da ido a birnin Urumqi fadar mulkin jihar Xinjiang ta Uygur mai cin gashin kai dake arewa maso yammacin kasar Sin.
Tawagar malaman dai ta fara ziyara a Urumqi ne tun daga ranar Lahadi 8 ga watan nan, bisa gayyatar gwamnatin jihar. Tana kuma karkashin jagorancin Ali Rashid Al Nuaimi, shugaban majalissun al’ummar musulmi na duniya.
Kaza lika tawagar ta hallara malamai daga hadaddiyar daular Larabawa, da Saudiyya, da Masar da Syria, da Bahrain, da Bosnia da Herzegovina. Sauran su ne Tunisiya, da Serbia, da Sudan ta kudu, da Mauritania, da Indonesia, da Kuwait, da Jordan da kuma Oman.
Bayan isar malaman Urumqi, sun ziyarci wuraren tarihi da dama, da kuma wuraren gudanar da ibada, inda suka nuna gamsuwa da yadda kasar Sin ta yaki ayyukan ta’addanci, da kare al’adun gargajiya da ba na kayayyaki ba na “Twelve Muqam”, da nasarar da kasar ta cimma karkashin shawarar nan ta ziri daya da hanya daya.
Bayan da suka nazarci yanayin zaman lafiya da lumana da daukacin al’ummun yankin ke ciki, mashawarci ga shugaban kasar Masar kan harkokin addinai Osama Sayyid Al-Azhari, ya amince cewa, manufar kasar Sin ta yaki da ta’addanci ta haifar da da mai ido, kuma abubuwan da suka gani a Xinjiang, sun isa darasi ga dukkanin kasashen duniya, a fannin yaki da ta’addanci.
Bugu da kari, kwararrun da kuma malamai, sun yi salloli tare da musulmin Xinjiang a cibiyar addinin musulunci ta jihar, sun kuma jinjinawa kokarin mahukuntan wurin, bisa kokarin su na tabbatar da damar al’umma ta gudanar da addinin da suka zaba. (Saminu Alhassan)