Tawagar Majalisar Dinkin Duniya da ke tallafa wa Kasar Libya (UNSMIL), ta sanar da kafa wani kwamitin sulhu na hadin gwiwa tare da majalisar shugabancin kasar da ke aiki a matsayin babbar kwamandan sojojin kasar ta Libya, a jiya Lahadi.
Kwamitin wanda aka kaddamar bayan kazamin fadan da ya barke a Tripoli, babban birnin kasar a ‘yan kwanakin da suka gabata, zai fi mayar da hankali ne wajen tabbatar da tsagaita wuta na dindindin, tare da mayar da hankali kan kare dukkan fararen hula, kana zai kuma amince da tsare-tsaren kula da tsaron Tripoli, kamar yadda sanarwar UNSMIL ta bayyana.
- Tsokaci Kan Yadda Wasu Matasa Ke Yin Aure Ba Tare Da Sana’a Ba
- Shugaban Kasar Sin Ya Jaddada Muhimmancin Samun Ci Gaba Mai Inganci Ta Fuskar Raya Wayewar Kai
Kazalika, sanarwar ta ce kwamitin wanda ke karkashin jagorancin babban hafsan hafsoshin sojin Libya, Mohammed Al-Haddad, ya nuna aniyar dukkan bangarorin rikicin na kauce wa ci gaba da tayar da zaune tsaye.
Tawagar UNSMIL ta sake nanata damuwar kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya kan rahotannin asarar rayukan fararen hula da rikicin baya-bayan nan ya haddasa a Tripoli, inda ta yi kira da a tsagaita bude wuta cikin gaggawa ba tare da gindaya wani sharadi ba.
Mummunan fada ya barke a sassa daban-daban na birnin Tripoli tsakanin dakarun da ke biyayya ga firaminista, Abdul-Hamed Dbeibah, da `ya`yan kakkarfar kungiyar masu dauke da makamai ta Stability Support Apparatus (SSA), da ke da nasaba da majalisar shugabancin kasar.
Majiyoyin tsaro sun ce rikicin ya yi sanadin mutuwar akalla mutane shida kafin sanar da tsagaita bude wuta a ranar Larabar da ta gabata.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp