Super Eagles sun koma Kano bayan tafiyarsu zuwa Libiya domin wasan neman cancantar shiga gasar AFCON ta 2025 bayan an fasa buga wasan sakamakon wlaƙancta su da aka yi.
An tilasta musu janyewa daga wasan saboda zargin cin zarafi da aka yi musu a filin jirgin sama na ƙasar Libiya, inda aka tsare ‘yan wasan da jami’an ƙungiyar na tsawon awanni daga Lahadi zuwa Litinin.
- An Kwaso ‘Yan Nijeriya 167 Da Suka Makale A Libya – NEMA
- Girgizar Kasar Maroko Da Ambaliyar Ruwar Libiya: Sama Da Rayuka 8,000 Sun Salwanta
CAF (Hukumar Kwallon Kafa ta Afirka) ta miƙa lamarin ga kwamitin ladabtarwa domin gudanar da bincike, inda ta tabbatar da cewa duk wanda aka samu da laifi na karya dokokin CAF zai fuskanci hukuncin da ya dace.
Super Eagles sun ƙauracewa wasan da aka shirya biyo bayan wannan matsala da suka fuskanta a wurin