Mai tsaron ragar kungiyar kwallon kafa ta Barcelona, Marc Andre ter Stegen ya buga wasanni 23 ba tare da kwallo ta shiga ragarsa ba a gasar La Liga a wannan kakar da ake bugawa.
Da wannan bajintar ya yi kan-kan-kan da tsohon mai tsaron ragar ta Barcelona, Claudio Brabo, wanda ya yi wa Barcelona wannan kwazon a kakar wasa ta shekara ta 2014 zuwa 2015.
A ranar Lahadin data gabata Barcelona ta ci abokiyar hamayyar ta watp kungiyar kwallon kafa ta Atletico Madrid 1-0 a filin wasa na Camp Nou a wasan mako na 30 a La Liga.
Kawo yanzu dai Barcelona ta buga wasanni 30, saura wasanni takwas a kammala kakar wasa ta Sifaniya ta 2022 zuwa 2023 wanda ake ganin kungiyar ta Barcelona za ta iya lashe wa.
Lokacin da Brabo ya yi wasanni 23 a La Liga kwallo bai shiga ragarsa, guda 19 aka ci a kakar, yanzu kuma tara ne suka shiga ragar kungiyar Nou Camp karkashin mai tsaron raga Ter Stegen, dan asalin kasar Jamus.
Ter Stergen ya fara da 0-0 a fafatawa da Ballacano ranar 13 ga watan Agusta a wasan farko da bude La Liga ta kakar nan sannan ranar 26 ga watan Afirilu, Barcelona ta ziyarci Rayo Ballacano, inda suka buga wasa na biyu a La Liga a tsakaninsu a bana.
Barcelona tana mataki na daya a kan teburin La Liga da maki 79, wadda ta ci karawa 26 da canjaras hudu aka doke ta wasa biyu a bana a La Liga haka kuma Barcelona ta ci kwallo 54 aka zura mata tara a raga a wasannin da ake yi a kakar nan.