TETFund ta sanar da dakatar da tallafin karatu zuwa ƙasar waje na shirin tallafin karatu ga Malamai (TSAS) daga ranar 1 ga Janairu, 2025. Wannan mataki ya biyo bayan tsadar kuɗin karatu a ƙasashen waje da kuma matsalar guduwar ɗaliban da ake bai wa tallafin.
- Ɗaliban Cyprus: Zamfara Ta Samar Wa Ɗalibanta ‘Yanci Da Ke Karatu A Gida Da Ƙetare
- Dokokin Gyaran Haraji Sun Tsallake Karatu Na Biyu A Majalisa
A cewar Abdulmumin Oniyangi, Daraktan hulɗa da jama’a na TETFund, waɗanda tuni suka fara karatu a ƙasashen waje za su ci gaba da amfana da tallafinsu har zuwa ƙarshen shirin. Ya ce dakatarwar za ta rage matsin lamba kan kuɗin canjin ƙasar waje, ƙara jari a cibiyoyin ilimi na Nijeriya, da kuma ƙaruwa a yawan masu amfana da tallafin.
TETFund tare da haɗin gwuiwa da NUC na aiki don aiwatar da sabbin dokokin ilimin duniya inda manyan jami’o’i daga ƙasashe kamar Birtaniya, da Amurka, da Malaysia za su haɗa kai da jami’o’in Nijeriya don samar da kwasa-kwasai masu inganci kamar na ƙasashensu. Wannan mataki zai taimaka wajen bunƙasa ilimi a cikin gida.
SEO Keywords:
TETFund, tallafin karatu, TSAS, karatun waje, ilimi a Najeriya, d
akatarwa.