Yau Alhamis ne jagorar mahukuntan yankin Taiwan na kasar Sin Tsai Ing-wen, ta gana da kakakin majalisar wakilan kasar Amurka Kevin McCarthy, yayin da Amurka ta baiwa jami’ar damar bi ta cikin Amurka, a hanyarta ta yin wani bulaguro.Â
Wannan ne karo na 2 da Amurka da Taiwan suka hada hannu wajen daukar matakan takala ta fuskar siyasa, bayan Nancy Pelosi ta ziyarci Taiwan a bara. Abin da Amurka ta yi ya saba wa ka’idar kasar Sin daya tak a duniya, da sanarwoyi 3 wadanda Sin da Amurka suka amince da su bisa hadin gwiwa, ya kuma illata ikon mulkin kasar Sin, da cikakkun yankunan kasar Sin, ya kuma sake aikewa wa ‘yan a-ware masu neman ‘yancin Taiwan munanan sakonni.
A hannu guda kuma, kasashen duniya sun kara gane cewa, mahukuntan Taiwan karkashin shugabancin DPP, suna kara yunkurin hada hannu da Amurka, yayin da wasu Amurkawa suke neman amfani da Taiwan wajen sarrafa akalar Sin, lamarin da ya kasance ainihin dalilin da ya sa ake rura wuta tsakanin gabobi 2 na mashigin tekun Taiwan.
Batun Taiwan, babbar moriyar kasar Sin ce mai matukar muhimmanci, kuma tushe ne na huldar da ke tsakannin Sin da Amurka ta fuskar siyasa, kana kuma shi ne jan-layi na farko da ba zai yiwu a tsallaka shi ba, a dangantakar Sin da Amurka. Kaza lika matakan da Amurka ta dauka, da kuma kalamanta, sun sake saba wa alkawarin da ta yi na bin ka’idar kasar Sin daya tak a duniya. Amurka tana ta daukar matakan takala.
Taiwan, yanki ne na kasar Sin. Al’ummar kasar Sin ne kadai suke da ikon daidaita batun na Taiwan. Makarkashiyar da Amurka da Taiwan suke kullawa, ba za ta sauya tarihin Taiwan na kasancewar bangaren kasar Sin ba, ba za ta murde gaskiya ba, ba za ta hana dinkuwar kasar Sin baki daya ba, ba za ta hana yawancin kasashen duniya su amince, da kuma goyon bayan ka’idar kasar Sin daya tak a duniya ba.
Tun tuni kasar Sin ta bayyana kin yarda da hada hannu tsakanin Amurka da Taiwan, kuma za ta mayar da martani. Babu wanda ya isa ya raina kudiri, da karfin da Sinawa suke da shi na kare ikon mallakar kasa da cikakkun yankunanta. (Tasallah Yuan)