Mataimakin Shugaban Kasa Sanata Kashim Shettima ya bayyana cewa shugaban Kasa Bola Ahmad Tunibu Masoyin Arewa da ‘yan arewa ne , ba kamar yadda wasu ke juya zance da cewa shi makiyin arewa ne ba.
Sanata Kashin Shettima ya bayyana haka ne a lokacin da ya karbi makoncin wasu ‘yan jaridu na arewacin Nijeriya a ofishinsa da ke fadar Shugaban Kasa, a Abuja.
- Zanga-zanga: Gwamnatin Kano Ba za Ta Amince Da Barnata Dukiyar Al’umma Ba
- Zaben Kananan Hukumomi: Za A Yi Wa ‘Yan Takara Gwajin Kwaya A Kano
Ya kuma bayyana cewa babu abin da gwamnatin suke buƙata a halin yanzu kamar goyon baya domin su samu damar shimfida ayyukan alheri ga al’ummar Nijeriya.
“Maganar cewa shugaba Bola Tinubu ba ya san mutanen arewa ko addinin Musulmi ba gaskiya ba ne, idan aka duba irin muƙaman da ya ba da a gwamantinsa musamman a manyan ma’aikatu da hukumomin gwamnati.” In ji shi.
Sanata Kashim Shattima ya yi ƙarin haske game da zanga-zangar da wasu matasa suke shirin yi, inda ya bayyana cewa dokar ƙasa ta ba su dama, sai dai ya ce babu wani abu a cikinta da ya wuce koma baya.
A cewarsa, akwai bukatar kafafen yaɗa labarai a wannan lokaci su sanar da al’umma cewa yin zanga-zanga a kan tituna ba zai kawo ci gaba a arewa ba.
“Yau ɗin nan, idan aka ce za a yi wannan zanga-zanga Allah kaɗai ya san irin asarar da za a tafka, duk da cewa ‘yan ƙasa suna da hakkin yin ta, amma matsala wasu marasa kishi na iya canza mata manufa” in ji Shettima.
Ya ƙara da cewa , alƙaluma sun nuna irin yadda shugaban ƙasa ya raba muƙamai a hukumomin ƙasar nan, musamman muhimman wurare da suka haɗa ma’aikatar gona da tsaro da harkar sadarwa da kiwon lafiya da sauransu.
Mataimakin shugaban kasar ya ce wannan gwamnati tana da kyakkyawar tanadi da ta yi wa ‘yan ƙasa domin inganta rayuwar mutanen arewa ta hanyar ɓullo da wasu tsare-tsare don tunkarar matsalar da yankin yake fuskanta.
Sanata Kashin Shettima ya ba da misalin da ƙirƙirar sabuwar ma’aikatar bunƙasa noma da kiwo, haka na nuna irin yadda shugaba Tunibu ke kaunar arewa, amma wasu na juya labarin da cewa Tunibu makiyin arewa ne.
Kamar yadda Sanata Kashin Shettima ya jefa tambaya inda ya ce wane ne ya sanya hannu a kan dokar hukumar farfaɗo da yankin arewa maso yamma? Kuma wane ne ya kirkiri ma’aikatar bunƙasa noma da kiwo?
Ya ce wannan shugaban ne dai ya amince da a ƙaddamar da tsarin yin amfani da matakin soja da kuma na diplomasiya domin tunkarar matsalar tsaro a arewa maso yamma da zai taimaka wajen warware ta.
Ya ƙara da cewa ta hanyar ɓullo da sabon shirin ECOSYSTEM ga waɗanda iftila’in hare-haren ‘yan bindiga ya shafa, wannan shirin zai inganta rayuwar ‘yan arewa.
Sanata Kashin Shettima ya roki ‘yan jaridu da su haɗa kai su zama tsintsiya maɗaurinki ɗaya wajen samar da ci gaba a arewacin Nijeriya, ya ce wannan gwamnati tana buƙatar addu’o’i a irin wannan lokaci domin samun nasara, amma yanzu ba lokacin zanga-zanga ba ne.
“Mu a nan arewa muna buƙatar bunƙasa ayyukan ci gaba waɗanda suke da mahimmancin a Nijeriya, saboda haka ba zamu kyale abubuwa su lalace ba” inji shi
Kazalika Sanata Kashin Shettima ya yi kira ga ‘yan jaridu na arewacin Nijeriya da su faɗakar da al’umma irin manyan muƙaman da shugaba Tunibu ya bai wa ‘yan arewa a gwamantinsa domin a bunƙasa ta.
Daga ƙarshe mataimakin shugaban ƙasan ya yi kira ga ‘yan arewa da su goyi bayan gwamnati mai ci yanzu domin a samu cigaba mai ɗorawa.