Shugaban Ƙasa Bola Tinubu, ya amince da ƙirƙirar dakarun daji masu makamai domin fatattakar masu aikata laifuka da ke ɓuya a dazukan Nijeriya.
Mai ba shi shawara kan harkokin yaɗa labarai, Sunday Dare, ya ce sabbin dakarun za su samu horo na musamman tare da ba su makamai.
- ECOWAS Na Fuskantar Matsala Saboda Rashin Kyakkyawan Shugabanci – Bala Mohammed
- ’Yan Bindiga Sun Sace Mutane 200 A Mazaɓa Ta A Zamfara – Ɗan Majalisar Tarayya
Ayyukansu shi ne yaƙar ‘yan ta’adda, masu garkuwa da mutane da sauran miyagun mutane a dazukan da ke faɗin ƙasar nan.
Gwamnatin Tarayya da ta jihohi za su haɗa gwiwa wajen ɗaukar ma’aikata, yayin da Ofishin Mai Bai Wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Tsaro da Ma’aikatar Muhalli za su jagoranci aiwatar da shirin.
Wannan mataki na daga cikin shirin gwamnatin Tinubu na inganta tsaro da kare ƙasa.
Shirin zai kuma samar da dubban guraben aikin yi ga matasa, wanda hakan zai rage rashin aikin yi a ƙasar.
Mutanen karkara da manoma da suka fi fama da matsalolin tsaro za su fi amfana da wannan mataki.
Shugaba Tinubu ya jaddada cewa ba za a bar masu aikata laifuka suke cin karensu ba babbaka ba.
Ya ce gwamnati za ta wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a ko ina a cikin Nijeriya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp